A yayin da al’ummar Musulmi ke shirye-shiryen shiga watan Azumin Ramadan, Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam ta jaddada buƙatar haɗin kai da dai...
A yayin da al’ummar Musulmi ke shirye-shiryen shiga watan Azumin Ramadan, Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam ta jaddada buƙatar haɗin kai da daidaito a tsakanin malaman addinin Musulunci.
Shugaban JNI, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi bayani dalla-dalla a wajen taron shekara-shekara da ake gudanarwa kafin Ramadan da aka yi ranar Litinin a Kaduna.
Matattarar Labarai ta ruwaito cewa taron ya kasance da taken; ‘Yadda Kafafen Sada Zumunta Ke Kawo Cikas Ga Haɗin Kan Malamai Masu Tafsiri Da Wa'azi’.
Sarkin Musulmi ya ce, “Dole ne mu haɗa kan Musulmi a ƙarƙashin inuwa ɗaya.
"Muna iya samun bambance-bambance kan yadda muke ganin abubuwa da yadda muke fahimtar abubuwa."
Sai dai ya buƙaci Musulmi su yi magana da kuma yi wa Musulunci aiki, yana mai cewa, “Wannan ya zama wajibi a rayuwar duniya.
"Bai kamata mu bar bambance-bambancen da ke tsakaninmu ya raba kanmu har ta kai ga zagin junanmu ba," inji shi.
A cewarsa, babu wanda ya ke da ikon sanin komai, inda ya ƙara da cewa, "Duk abin da ka ke tunanin ka sani, wani ya fi ka sani."
Sarkin Musulmi ya ce, ta hanyar bin ƙa’idoji da ɗa’a masu kyau, malamai za su iya inganta kyakkyawar ɗabi'a a watan Ramadan ga kowa da kowa.
Tun da farko a nasa jawabin, Farfesa Khalid Aliyu, babban sakataren JNI, ya bayyana muhimmancin mutunta kai ga malamai da kuma buƙatar malamai su bi ƙa’idoji da ɗa’a.
Aliyu ya jaddada cewa malaman Musulmi suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen bunƙasa haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin al'ummar Musulmi.
Sai dai ya ce, za a iya cimma hakan ba ne kawai idan malamai suka yi riƙo da kyawawan ɗabi’u na ilimi, tare da nisantar ra’ayi na ƙashin kai, da yaɗa farfagandar mazhaba.
Aliyu ya kuma buƙaci malamai da su kasance masu amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaɗa ayyukan ƙwarai.
Ya ce, “Saboda bunƙasuwar kafafen sada zumunta, malamai sun samu sauƙi wajen yaɗa koyarwarsu da kuma cuɗanya da sauran jama’a.
"Duk da haka, wannan kuma ya haifar da yaɗa labaran ƙarya da zagin wasu aƙidu da neman rarrabuwa."
Aliyu ya ce, JNI ta kafa ƙa’idojin Tafsiri, wanda ya jaddada buƙatar malamai su yi riƙo da kyawawan ɗabi’u na ilimantarwa tare da kaucewa yaɗa farfagandar bangaranci.
Ya kuma yi kira ga malamai da su fifita hikima da tawali’u a cikin koyarwarsu.
“Wannan ya haɗa da guje wa haifar da rikice-rikice, inda ya kamata a mayar da hankali kan isar da saƙonnin gaskiya.
"Akwai muhimmanci kan haɗin kai da mutunci a tsakanin malaman Musulmi."
Matattarar Labarai ta ruwaito cewa, taron ya samu halartar sarakunan masu daraja ta ɗaya, malaman addinin Islama, da malamai daga sassan ƙasar nan.

No comments