Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar 'IPAC' Ta Koka Kan Yadda 'Yan Siyasa Ke Kalaman Ɓatanci A Tsakaninsu a jihar Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Shugaban haɗakar Jam'iyyu ta ƙasa reshen jihar Kano, IPAC, wanda kuma shi ne shugaban jam'iyyar ZLP na j...

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Shugaban haɗakar Jam'iyyu ta ƙasa reshen jihar Kano, IPAC, wanda kuma shi ne shugaban jam'iyyar ZLP na jihar Kano, Alhaji Isah Nuhu Isah Ɗanfulani ya bayyana damuwa da nuna rashin jin daɗi game da yadda 'yan siyasa ke shiga kafafen yaɗa labarai suna ɓatanci ga junan su.

Yayin zantawa da wakilin mu a Kano cikin makon nan, Shugaban na IPAC ya yi nuni da cewa  wannan halayya ta saɓa wa mutuntaka da koyarwa ta addinin musulunci, kuma hakan ya saɓa tsari na zamantakewa da girmamawa da aka san jihar Kano da shi.

Ya ce, haƙioa wannan na nuna cewa 'yan siyasa  suna koyar da wata tarbiyya da ba daidai ba a cikin al'umma ta ƙoƙarin dasa munanan abubuwa  da zai cutar da siyasa.

Alhaji Isah Nuhu Isa Ɗanfulani  ya kuma bayyana  ce ba za su yarda su zuba ido suna ganin ana irin waɗannan munanan kalamai na ɓatanci da cin zarafi ba, domin ita siyasa ba ta gaji haka ba.

Ɗanfulani ya ce mu'amala mai kyau, ita ce siyasa, ba cin zarafi ba. Idan mutum ya yi wani abu a matsayinsa na mai mulki, kai kuma a matsayinka da ka yi mulki ka gama, abin da ka yi na daidai, sai a fito a faɗa, wanda ba na daidai ba, a fito a faɗa cikin girmamawa da mutuntaka.

 

No comments