A yau Asabar ne aka shirya za a gudanar da babban taron mahaddata Alƙur'ani, 'Qur'anic Convention', irin sa na farko a ƙasar...
A yau Asabar ne aka shirya za a gudanar da babban taron mahaddata Alƙur'ani, 'Qur'anic Convention', irin sa na farko a ƙasar nan, amma manazarta harkokin yau da kullum na ganin cewa sakamakon cece-kucen da ya biyo bayan shirin, dole ta sa a ɗage, ko aka janye taron.
A kwanakin baya BBC ta yi tsokaci da cewa an ɗage taron mahaddata al-Qur'anin ne har sai zuwa bayan watan Ramadana.
In dai ba a manta ba an saka ranar Asabar 22 ga watan Fabrairun nan na 2025 a matsayin ranar da za a yi taron, wanda ake sa ran zai samu mahalarta waɗannan mahaddata Alƙur'ani ne sama da dubu 60 daga ciki da wajen Nijeriya.
Wanin abu da ke ɗaure wa jama'a kai, shi ne, su masu shirya wannan taro, babu wanda ya fito ya shaida wa duniya dalili, ko dalilan d suka sabbaba aka ɗage wannan taro, domin hatta ita majiyar ta BBC ɗin, ba ta bayyana haƙiƙanin dalilin da ya sa aka ɗage taro ba da kuma yaushe ne sabon lokacin da za a yi taron a nan gaba ba, sai dai ta ce sai bayan Azumin Ramadan.
Kafin ɗage wannan taron dai, tuni allunan tallarsa suka cika manyan titunan birnin Abuja, kuma ya kankane kafafen watsa labarai da na zumunta, inda wasu ke yabo wasu kuma ke kushe shi.
Da ma tun kafin yanzu batun taron na mahaddatan ya janyo muhawara, inda wasu ke sukar kalmar da aka yi amfani da ita a farko ta "festival" da ke nufin "biki", sannan wasu ke dangantaka al'amarin da siyasa, wasu kuma suke kallonsa a matsayin wani abu baƙo a addinin Musulunci, wato Bidi'a.
Manufar taron dai kamar yadda shafin tsara taron ya ce shi ne fito da irin jajircewar da mahaddata Alƙur'ani suka yi shekara aru-aru.
"Al'ummar Najeriya daga sassa da ƙabila daban-daban na ƙasar sun sadaukar da rayuwarsu wajen haddace Qur'ani a ɗaruruwan shekaru," kamar yadda ya ke rubuce a shafin da ke tsara taron.
"Saboda haka wannan taron zai zama wani dandamali na karrama makaranta da marubuta Alƙur'ani mai girma. Sannan wata mahaɗa ce da ke nuna yadda al'adu da ƙabilun Nijeriya daban-daban ke karanta da mu'amala da Alƙur'ani da irin karin harshensu sannan bisa al'adunsu," In ji shafin.
Taron zai fito da irin jajircewa da ƙoƙarin mutanen da suka haddace da kuma waɗanda suke iya rubuta Alƙur'ani baki ɗaya.
Haka kuma taron zai tattara al'umma daga sassa da ƙabila daban-daban na Nijeriya da ke ma'amala da littafi mai tsarki.
Masu shirya wannan taro, suna bayyana cewa, wata manufa ta wannan taro ita ce sanya wa yara sha'awar haddace Alƙur'ani tun da ƙuruciyarsu, ta hanyar tallata irin nasarar da mahaddatan suka yi domin ganin al'adar haddar ta ɗore.
Sun kuma nuna cewa, a lokacin taron, za a fito da irin basira da kaifin hadda da kuma jajricewar da mahaddata ke da ita.
Sai dai duk da waɗannan hujjoji da masu shirya wannan taro suka kawo, masu suka ga abin, suna kawo hujja da cewa yawancin jagororin taron, mutane ne masu sukar duk wani abu da Manzon Allah bai zo da shi ba, wato Bidi'a. Amma a wannan, suka yi ruwa suka yi tsaki a ciki.
.jpeg)
No comments