Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Ƙaddamar Da Biyan Bashi Ga Mutum 1000 Na Gidan Yari

Daga Hussaini Yero, Gusau Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, yare da haɗin gwiwa da Hukumar Zakka da waƙaf, ta biy...

Daga Hussaini Yero, Gusau

Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, yare da haɗin gwiwa da Hukumar Zakka da waƙaf, ta biya wa mutane dubu ɗaya da a ke bin su bashi, waɗanda ke tsare a gidan gyaran hali da wajen Hukumomi da  masarautu goma Sha Tara da ke cikin jihar, tare da bayar da tallafin shinkafa da kuɗi ga marasa galihu domin taimakawa wajen rage raɗaɗin talauci da ake fama da shi a cikin jihar.

Babbar Mataimakiya ta musamman ga Uwar gidan gwamnan, Zahara'u Musa ce ta bayyana haka a takardar da ta sanya wa hannu ga manema labarai.

"A cewar ta, shirin na da nufin haɗa kan iyalai, da dawo da martaba, da kuma baiwa ɗaiɗaikun mutane damar dogaro da kai. 

Huriyya Dauda Lawal ta bayyana cewa kimanin mutane dubu ɗaya ne za su ci gajiyar wannan shirin na Tallafin basusuka da kayan Abinci da kuɗi.

Ta ce, "Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara ya umarci Hukumar Zakka da tantance waɗanda basusuka ya kai su gidan gyaran hali da ke faɗin Jihar domin biya masu. An kafa wani kwamiti a ƙarƙashin Grand Khadi, tare da Kwanturolan gidajen yari da Malamai, wanda aka ɗora wa alhakin daidaita basussuka da kuma taimakawa wajen ɗinke matsalar ma'aurata."

Bugu da ƙari, Huriyya Dauda Lawal ta bayar da tallafin kuɗi da buhunan shinkafa ga waɗanda suka ci gajiyar tallafin domin dogaro da kai, tare da buƙatar su da su guji karɓar lamuni domin kare mutuncinsu.

“Ina sanar da al’ummar jiharmu cewa mai girma Gwamnan Jihar Zamfara na ƙoƙarin ganin an rage wa marasa hali da marasa galihu raɗaɗin da suke ciki a faɗin Jihar,” Inji Huriyya.

 

No comments