Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mahaifina Ya Yi Mani Dukkan Gatar Da Uba Ke Ma Ɗansa -Chiroman Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Sabon Chiroman Kano DSP. Aminu Sanusi ya bayyana godiyar ga Allah bisa cika masa buri da ya yi na ba shi sarauta...

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Sabon Chiroman Kano DSP. Aminu Sanusi ya bayyana godiyar ga Allah bisa cika masa buri da ya yi na ba shi sarauta mai daraja, inda ya yi roƙon Ubangiji ya ba shi daman riƙe wannan amana da aka ba shi.

Ya kuma bayyana cewa mahafinsa mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi, duk wata gata ya yi masa, don haka babu abin da zai iya saka masa sai addu'a Allah ya ƙara masa lafiya da ɗaukaka, ya raba shi da Duniya lafiya.

Aminu Sanusi ya ce a matsayinsa na ma'aikacin tsaro, ko da babu rawani yana da kaki, sun yi aiki a Sakkwato da Legas, yadda za su yi aiki da ɗamara haka za su yi da rawani.

Chiroman Kano DSP Aminu Sanusi ya ce babu abin da za su ce ga ɗimbin jama'a sai godiya bisa ƙauna da soyayya, yadda suka nuna musu ƙauna, Allah ya nuna musu.

 

No comments