Daga Ibrahim Muhammad, Kano Hajiya Mariya Muhammad Sanusi, wacce ta ke Kaka ce ga sabon Chiroman Kano, DSP Aminu Sanusi, ta bayyana naɗin ...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Hajiya Mariya Muhammad Sanusi, wacce ta ke Kaka ce ga sabon Chiroman Kano, DSP Aminu Sanusi, ta bayyana naɗin da cewa rana ce mai farin ciki na tarihin da ya maimaita kansa. Ta ce, domin mahaifin su ya hau kan wannan matsayi, yayanta ma ya hau, kuma duk ba wanda ba su ji daɗin sa ba, yanzu ga shi jikan su ya zo ya hau wannan matsayi na Chiroman Kano.
Hajiya Mariya ta ce suna fata da yi masa addu'a Allah ya sa ya gaji halayen wanɗanda ya gada duk gaba ɗ ɗaya, daga mahaifi har wan su, ya ɗauki halayensu na son jama'a da zama da jama'a lafiya da riƙo da tafarkin Ubangiji.
Daga nan Hajiya Mariya Muhammadu Sanusi ta cewannan sarauta ta Chiroman Kano, duk wanda ya riƙe, to yana kambama ta, waɗanda suka riƙe ta duk sun ɗaukaka ta, ta zama tamkar kamar ita ce babba a Masarautar Kano.

No comments