Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gudunmawar Ambasada Yusuf Hassan Darma Ga Ci Gaban Al'ummar Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jama'a da dama musamman a Ƙaramar Hukumar Birnin Kano da sauran wasu daga Ƙananan Hukumomi a  Kano ta  Tsaki...

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Jama'a da dama musamman a Ƙaramar Hukumar Birnin Kano da sauran wasu daga Ƙananan Hukumomi a  Kano ta  Tsakiya na yaba wa irin   gudunmawar da Ambasada Alhaji  Yusuf Hassan Darma yake bayarwa a kowane lokaci wajen  tallafa wa bunƙasa ci gaban al'umma  a ɓangarori daban-daban.

Alhaji Yusuf Hassan Darma  ɗan kasuwa ne mai tausayi da jin ƙai, ganin irin halin ƙuncin rayuwa da al'umma ke ciki ya ƙara azama  yake tallafa musu a fannoni da dama da suka haɗa da  ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane maza da mata, musamman masu ƙaramin ƙarfi. Kamar yadda wani ɗan kasuwa, Alhaji Abubakar Kanavaro ya ke tabbatar da  hakan bayan wani rabon tallafi da  Yusuf Hasan Darma ya yi a Kumbotso.

Alhaji Yusuf Hassan Darma  sananne ne akan irin gagarumar gudummawa da ya bayar domin tabbatar da samun nasarar Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam, ba a  wannan karon ba kaɗai ba, tun daga takarar sa na zaɓen  2019.

Tun  daga yaƙin neman zaɓe da lokacin zaɓe har kaiwa ga nasara da aka yi a jam'iyyar NNPP, ya bada gudunmawa da yin sake yin tsayin dakan ganin an yi nasara a Shari'a har aka tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf.

Wannan ne ya sa mutane da dama suke kira ga Gwamnatin jihar Kano ta Alhaji Abba Kabir Yusuf da mataimakin sa Kwamared Aminu Abdussalam su yi duba da lura da irin gudumawar da wannan bawan Allah yake bayarwa da aljihunsa, domin irinsu ya kamata a jawo su a jiki, duk abin da za a yi na al'umma a damƙa musu, saboda za su isar da saƙon Gwamnati duk inda aka tura.

Da ga irin gudunmawa da Ambasada Alhaji Yusuf Hassan Darma ya bayar har da na sanya fitilu a mazabu 13 na ƙaramar hukumar Birnin Kano, yana  kuma raba tallafi ga bunƙasa ci gaban ilimi ta biya wa yara Kuɗin jarabawa da iyaye mata da matasa da jari na sana'o'i.

Malam Aliyu Mamman Mai Mari, ɗaya ne daga waɗanda ƙungiyar da yake jagoranta ta amfana da tallafin N500,000 daga Ambasada Alhaji Yusuf Hassan Darma, ya ce ba shi kaɗai ba, akwai ƙungiyoyi da dama da wasu suka amfana da kuɗaɗe kama daga N250,00 wasu 300,000 har sama da haka, kuma wannan tallafin da ya ba su cikin ikon Allah zai ba su dama na cika burin abin da suka sa a gaba su ma na tallafa wa al'umma.

Jama'a da dama suna kira ga shugabanni musamman Gwamnatin jihar Kano da sauran jagorori da yake dama sun san wa ne ne Ambasada Yusuf Hassan Darma da irin gudunmawa da yake baiwa al'umma daga aljihunsa ba tare da yana da wani muƙami a gwamnati ba, a duba a ba shi wani gwaggwaɓan muƙami da zai daɗa ƙarfafarsa wajen taimaka wa ci gaban al'umma.

No comments