Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sanata Barau Ya Yaba Wa Tinubu Kan Mayar Da Kwalejojin Ilimin Zariya da Kano Zuwa Jami'o'in Ilimi Na Tarayya

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan sauya Kwalejojin Ilimi na Tarayya...

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan sauya Kwalejojin Ilimi na Tarayya da ke Kano da Zariya zuwa Jami’o’in Ilimi na Tarayya.

Shugaba Tinubu ya amince da mayar da kwalejojin biyu zuwa jami’o’in ilimi na tarayya domin inganta harkar ilimi a ƙasar nan daidai da ajandar "inganta Nijeriya".

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fitar da wasu takardu da ke amincewa da sauya tsarin cibiyoyin ilimin.

Sanata Barau, a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir ya fitar, ya ce 

sauya kwalejojin ba wai kawai zai ƙara inganta karatunsu ba ne, har ma da inganta ilimin malamai da kuma habaka koyarwa a ƙasar nan.

Sanata Barau, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban kakakin majalisar ECOWAS na farko, ya taya shugabanni, ma’aikata, ɗalibai, da ɗaukacin al’ummomin cibiyoyin murna, inda ya buƙace su da su ci gaba da ɗaukaka darajar ilimi.

Ya kuma bayyana fatansa cewa, za a yi la’akari da wannan ƙudiri nasa na mayar da Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Technical), Bichi, zuwa Jami’ar Ilimi ta Tarayya (Technical), Bichi, don ba da horon da ake buƙata ga matasan Nijeriya.

No comments