A ranar 21 ga watan Satumbar kowacce shekara rana ce da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Zaman Lafiyata Duniya. Ranar na may...
A ranar 21 ga watan Satumbar kowacce shekara rana ce da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Zaman Lafiyata Duniya.
Ranar na mayar da hankali wajen kawo mafita kan tashe-tashen hankula a ke fama dashi na banbancin addini yare da kuma ƙabilai a faɗin duniya.
Sai dai binkin a bana ya zo lokacin da ake tsaka da fama da matsalar rashin tsaro a sassan ƙasar nan musamman na hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane.
Shugaba kuma Babban Kwamandan Ƙungiyar ‘Yan Sintiri ta Nijeriya (VGN), Kaftin na sojan ruwa (mai ritaya), Abubakar Umar Bakori ya shawarci al'ummar Nijeriya da su zauna lafiya da juna, kuma su guji duk wata hanyar tashin hankali.
Kwamandan ya yi wannan kiran ne a yayin tattaunawarsa da manema labarai domin tunawa da Ranar Zaman Lafiya ta Duniya a Jihar Kaduna, ranar Asabar.
Ya yi nuni da cewa zaman lafiya da juna shi ne abu mafi muhimmanci domin tabbatar da ci gaba cikin sauri a cikin al’umma.
Kaftin Bakori ya ƙara cewa, "Babu abin da tashin hankali ke haifarwa face talauci da yunwa, don haka ya kamata mu zauna lafiya, mu daina kashe kawunanmu".
Ya ce, "akwai lokacin da mu ke cikin talauci a arewacin Nijeriya, amma duk faɗin ƙasar ana yi mana kallon cewa mu ne masu kuɗin Nijeriya saboda muna zaman lafiya da juna. Don haka, ya kamata mu tashi tsaye mu dawo da wannan zaman lafiyar".
Ya ci gaba da cewa, "Muna da yara a cikin ƙungiyar ’yan sintiri fiye da mutum miliyan ɗaya, waɗanda a shirye su ke su shiga duk inda aka umarce su a lungu da saƙo domin tsare rayukan al'umma".
Ya ce, waɗannan 'yan sintiri sun san ko ina kamar yadda ’yan ta'adda suka sani, domin kowannen su na aiki ne a mahaifarsa, ba a kai mutum wani wuri na daban.
"Me ya sa gwamnati ba za ta yi amfani da waɗannan yara ba wajen magance ’yan ta'adda? Sai dai ka ji gwamnoni na fitowa suna cewa sun kashe maƙudan kuɗaɗe wajen ƙaddamar da wata ƙungiyar tsaro, maimakon taimaka wa waɗannan jaruman yara waɗanda ba sa buƙatar ko kobo daga hannun wani," in ji Bakori.
Kaftin Bakori ya sha alwashin cewa, idan har ’yan sintiri sun samu goyon baya da kayan aikin da su ke buƙata, to tabbas za a nemi ’yan ta'adda a rasa, ya ce "domin su (’yan bindiga) ba aljanu ba ne, mutane ne".
Ya ce, "Idan har da gaske gwamnati na son kawo ƙarshen matsalar tsaro, ya kamata ta ƙarfafa waɗanan yara, domin a shirye su ke su tunkari ’yan ta'adda."
"Ya kamata a lura cewa waɗanan yara yawancin su manoma ne, ’yan kasuwa da kuma ’yan farauta, don haka ba wai suna neman aikin gwamnati ba ne.
Kaftin Abubakar Bakora ya jaddada buƙata da muhimmancin zaman lafiya, inda ya ce a shirye yake ya yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya, amma dole sai da taimakon gwamnati.
No comments