Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Haɗe Masarautun Kano Da Dawo Da Sarki Sanusi, Kare Kimar Masarautar Ne -Gambo Ɗanpass

Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana sake dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II da gwamnatin Jihar Kano ƙarpashin jagorancin Injiniya Abba Kab...


Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An bayyana sake dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II da gwamnatin Jihar Kano ƙarpashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta yi da cewa adalci ne da sanin ya-kamata da dawo da kima da darajar Masarautar Kano. 

Ɗaya daga cikin Dattawan 'yan kasuwa a Jihar Kano, Basarake, Ɗan Saran Kano, Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpass ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano cikin makon nan.

Alhaji Gambo ya ce Sarkin Muhammad Sanusi, a lokacin da yake sarautar Kano a baya ya yi mutuƙar taimakawa wajen haɓaka Kasuwancin mutane, musamman baƙi daga ƙasashen Duniya sun riƙa zuwa Kano, wanda hakan ya jawo hankalin masu zuba jari da Kuma  bunƙasa Kasuwanci.

Ya ci gaba sa cewa, dama an yi amfani ne da wata  dama ta son rai da bai dace ba wajen raba masarautar Kano saboda wata manufa ta siyasa, wanda duk da a lokacin mutane daga ciki da wajen ƙasar nan sun yi gargaɗi ga yin hakan bai kamata ba, amma aka yi biris.

Ya ce, zuwan wannan Gwamnati da 'yan 
 majalisar Kano suka duba Dokokin yadda aka ƙirƙiri sabbin masarautun suka ga akwai kuskure suka gyara suka haɗe masarautun zuwa ɗaya kamar yadda ake a baya, dama kuma al'ummar Kano da dama suna kiraye-kiraye akan a dawo da Sarkin Muhammad Sanusi.

Daga nan sai Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpass ya yi kira ga al'ummar Jihar Kano akan su ci gaba da baiwa Gwamnati haɗin kai da goyon baya, su kauce wa duk wani mai ƙokarin haddasa fitina a tsakanin al'umma saboda son ransa.

Da ya juya kan cika Shekara ɗaya na Gwamna Abba Kabir Yusuf akan kujerar mulki kuwa, Ɗanpass cewa ya yi al'ummar Kano sun mori ayyuka a fannoni da dama, tun daga inganta harkar ilimi da kula da lafiya, da gina ci gaban al'umma da tallafa wa Matasa da Mata, da gina hanyoyi da abubuwa da dama.

Ya ce duk da cewa Gwanna ya samu tsaiko a shari'a da aka yi, amma hakan bai hana shi ya gudanar da muhimman ayyuka na gina ci gaban al'umma  ba.

No comments