Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta haramta duk wani nau'i na hawan Sallah, musamman babbar sallah da ke tafe a Birni...
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta haramta duk wani nau'i na hawan Sallah, musamman babbar sallah da ke tafe a Birnin jihar
Mai magana da yawun Rundunar 'yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da haka a shafin sa na Facebook, inda ya ce sun É—auki wannan matakin ne sakamakon turka-turkar da ake fama da ita game da masarautar Kano.
Kakakin ya ce, kafin ɗaukar wannan matakin, sun an tuntuɓi masu ruwa da tsaki a jihar domin wanzar da zaman lafiya a faɗin jihar.
A wata sabuwa kuma, a yau ɗin nan ne dai wata kotun tarayya da ke jihar ta bayyana cewa tana da hurumin sauraren ƙara kan masarautar jihar, wacce Sarki Aminu Ado Bayero ya shigar
No comments