Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

BIKIN SALLAH: Yadda Kiristoci Suka Gyara Wa Musulmi Filin Idi A Kaduna

Daga Musa Muhammad  A wani gagarumin baje koli na haɗin gwiwa tsakanin mabiya addinai, wani Fasto ya jagoranci Ƙungiyar Kiristoci domin haɗa...


Daga Musa Muhammad 

A wani gagarumin baje koli na haɗin gwiwa tsakanin mabiya addinai, wani Fasto ya jagoranci Ƙungiyar Kiristoci domin haɗa kan Musulmi wajen tsaftace filin Sallar Idi, a wani ɓangare na bikin Sallah a Ƙaramar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.

Wannan shiri dai an yi shi ne domin samar da zaman lafiya, tattaunawa tsakanin addinai, haƙuri da juna, fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban na yankin da ma jihar baki ɗaya.

Fasto Yohanna Buru, Babban mai sa ido kuma faston cocin Christ Evangelical and Life Intervention, ya shirya tawagar Kiristocin da suka je filin Sallar Idi domin tsaftace filin a shirye-shiryen bukukuwan Sallah mai zuwa da ke tafe nan da 'yan kwanaki.

Tawagar Kiristocin ta je garin Kasuwar Magani da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna inda suka haɗa kai da ’yan uwa Musulmi domin share filin Sallar Idi.

Wannan ƙoƙari na haxin gwiwa da ya haɗa da limaman Coci, an yi shi ne don samar da yanayi mai tsafta ga Musulmi wajen yin addu’a, ta yadda za a samar da zaman lafiya da haɗin kai a yankin.

Da yake jawabi, Fasto Buru ya jaddada cewa Musulmi da Kirista duka suna bauta wa Allah ɗaya ne kuma suna da littattafansu masu tsarki, Bebul na da kuma Alkur’ani.

Tare da Rabaran Danjuma Mazadu da wasu matasa Kiristoci, ya ce “Mun zo nan ne domin tallafa wa ’yan uwanmu da su sare ciyayi da kuma share duk wani datti da ke kewaye da filin da nufin samar da zaman lafiya da haɗin kai.

Yayin da yake taya al’ummar Musulmi a faɗin duniya murnar Sallah, ya yi kira ga masu hannu da shuni da su riƙa tunawa da marayu da zawarawa da mabaratan tituna a lokacin bukukuwan.

Aikin share filin wanda ya ɗauki tsawon sa'o'i da dama, ya baiwa Kiristoci da Musulmi damar shiga tattaunawa, da yin musanyar abokantaka, da kuma tattauna hanyoyin ƙarfafa juriya da fahimtar addini.

"Muna godiya ga 'yan uwanmu Musulmai bisa damar da aka ba mu na tallafa musu wajen tsaftace yankin masallaci."

Ya kuma miƙa gaisuwa ga Sarkin Musulmi, Sheikh Dahiru Bauchi, Sheikh Ibrahim Yakubu El-Zazzaky, da Sheikh Ahmed Mahmud Gumi, Sheikh Salihu Mai-barota, da Muhammad Sanusi, Sarkin Kano.

A nasa jawabin, Rabaran Danjuma Mazadu Makama na Kasuwar Magani ya ce sun zo masallacin ne domin yin addu’o’i da kuma taimakawa al’ummar Musulmi wajen tsaftace muhalli a shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Sallah mai zuwa nan da kwanaki kaɗan.

Shi ma wani shugaban matasan Kirista a yankin Johathan Peter ya ce sun shafe shekaru da dama suna yin haka domin kara kyautata alaƙa tsakanin Kirista da Musulmi a cikin al’umma.

Da yake mayar da martani, Imam Akilu Mohammed, babban limamin garin Kajuru, ya bayyana farin cikinsa kan yadda fastoci da sauran mabiya addinin Kirista suka yi, yana mai cewa, abin da suka aikata ya cancanci a yi koyi da su.

“Wannan ba shi ne karo na farko da ’yan uwanmu Kiristoci suke taimaka mana mu sare ciyawa da ke kewaye da mu ba. A shekarar da ta gabata sun ba mu goyon baya wajen share harabar masallacin, wanda hakan ya taimaka wajen samar da zaman lafiya da fahimtar addini a yankin.

Ya kuma yi nuni da cewa, a wani iftila'i da ya faru a baya-bayan nan da guguwar iska da ta lalata cocina da masallatai, al’ummomin biyu sun ziyarci juna tare da yin addu’o’in neman tsari daga Allah Maɗaukakin Sarki domin kauce wa faruwar hakan a nan gaba.

No comments