Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ba A Naɗa Mataimakin Mai Tafsiri A Masallacin Sultan Bello Da Wata Manufa Ba -Jama'atu

Daga Musa Muhammad Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam, JNI ta ƙasa ta bayyana cewa Masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarki, Kaduna ba na zur...

Daga Musa Muhammad

Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam, JNI ta ƙasa ta bayyana cewa Masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarki, Kaduna ba na zuriyar Marigayi Shaikh Abubakar Gumi ko na wani mutum ba ne, na al’ummar Musulmi ne gaba ɗaya, wanda ke ƙarƙashin kulawar ta.

Ta kuma ce, naɗin mataimakin mai gabatar da Tafsiri a masallacin da aka yi, an yi shi ne bisa ƙa'ida, ba wai an yi ne don a muzguna wa wasu ko wanitum ba. 

JNI ta ce, Limamai, mataimakan su, masu wa'azi da mataimakin sa, da duk masu kula da harkar masallacin, duk suna ƙarƙashin kulawar ta ne, na abin da ya shafi albashi da sauran hudindimun masallacin.

Sakataren gudanarwa na ƙungiyar ta JNI, Malam Yusuf Bida ne ya bayyana haka a ranar Litinin a ofishin ta da ke Kaduna a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai dangane da wani rubutu da aka yi a shafukan sada zumunta kan naɗin wanda zai zama mataimaki ga Dr Ahmad Gumi wurin gabatar sa Tafsiri.

Rubutun wanda ɗaya daga cikin ɗaliban Sheikh Dr Ahmad Gumi ya yi, ya yi iƙirarin cewa sabon mataimakin mai gabatar da Tafsiri a masallacin, ba mabiyi ne ga makarantar Marigayi Shaikh Abubakar Gumi ba.

A rubutun, an kuma bayyana cewa wasu mutane ne da ba su da alaƙa da masallacin da koyarwar Marigayi Shaikh Abubakar Gumi suka yi naɗin mataimakin, don haka ba za su amince da shi ba.

Haka kuma a cikin waccan takarda ta ɗalibin Dr Gumin, sun jawo hankalin mabiyan su a duk faɗin ƙasar nan da su yi watsi da wannan naɗi na mataimaki da aka yi wa Gumin, inda suka yi zargin cewa ba a taɓa naɗa wani mataimaki ba, kafin hawan Dr Gumi kan kujerar. 

Don haka sai ƙungiyar ta Jama'atu ta ce, Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ne da kansa ya sanya hannu a takardar naɗin Dr Muhammad Jamil Salis a matsayin mataimakin mai tafisiri a wannan masallaci. 

"Muna so mu yi cikakken bayani game da naɗa mai Tafsiri a masallacin Sultan Bello. Lokacin da Allah ya yi wa Shaikh Abubakar Gumi rasuwa, Marigayi Shaikh Halliru Binji daga Sakkwato ne aka naɗa domin ci gaba da gudanar da Tafsiri a ranar 25 ga watan Janairun 1993,  har ya amince, amma kafin Azumi ya zagayo, sai Allah ya yi masa rasuwa. 

"Bayan rasuwar Farfesa Halliru Binji ne sai aka naɗa Marigayi Shaikh Lawal Abubakar, inda ya kwashe shekaru yana gudanar da Tafsirin, bayan rasuwar sa sai aka naɗa Limamin masallacin Kwalejin Rimi da ke Kaduna, Marigayi Shaikh Umar Hasan. 

Bayan ya kwashe kimanin shekaru biyu yana gabtar da Tafsirin, sai aka yi shawarar sanya abin cikin tsari, inda aka naɗa Shaikh Dr Ahmad Gumi a matsayin wanda zai gudanar da Tafsirin, sakamakon rahoton wani kwamitin da Kanar Hamid Ali ya jagoranta," in ji Jama'atu. 

Don haka sai Bida ya tabbayar wa duniya cewa, har yana rantsuwa, ba an yi wannan naɗi na mataimakin mai Tafsirin ba ne da wata mummunar manufa, an yi ne don Allah, don ɗaukakar musulunci. 

A cewar Malam Bida, an yi wancan rubutun ne da nufin tunzura jama’a da haifar da hargitsi a cikin masallacin da aka daɗe ana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Don haka sai Malam Yusuf Bida ya yi ƙarin haske da cewa naɗin Limamai da mataimakan su a masallacin Sultan Bello, haƙƙi ne na Jama'atu, wanda ta daɗe tana yi shekara da shekaru.

Ya ƙara da cewa, bayan an gudanar gwaji na ilimi da sauran fannoni, sai aka cimma matsaya na naɗa wanda ya fi kowa cancanta a matsayin Limami ko mataimakinsa ko mai gabatar da Tafsiri a masallacin. “Da haka ne aka naɗa Shaikh Dr Ahmed Gumi, wanda a yanzu shi ne ke gabatar Tafsiri a masallacin.

Bida ya kuma yi kira ga jami’an tsaro a jihar da hukumar kula da masallacin da su gaggauta ɗaukar ƙwararan matakai a kan duk wani abu da ke ƙoƙarin haifar da rikici a cikin masallacin.

No comments