Kamfanin Sadarwa na MTN a Nijeriya ya fitar da sanarwa inda ya nemi afuwar abokan hulɗarsa saboda rashin ƙarfin 'network' da suke fu...
Kamfanin Sadarwa na MTN a Nijeriya ya fitar da sanarwa inda ya nemi afuwar abokan hulɗarsa saboda rashin ƙarfin 'network' da suke fuskanta.
An tattaro cewa da alama matsalar ta shafi ayyukan kira da kuma na intanet, lamarin da ya janyo katsewar sadarwa ga miliyoyin masu amfani da yanar gizo.
Masu amfani da layukan MTN sun shiga dandalin sada zumunta na yanar gizo suna bayyana kokensu, inda suka bayyana takaicinsu kan katsewar intanet da kuma yadda yake tasiri a harkokinsu na yau da kullum.
Lalacewar wayoyin ƙarƙashin teku a sassan gabashi da yammacin Afirka lamarin ya sa ƙasashen Afirka da dama fuskantar gagarumar matsalar katsewar sadarwar intanet a ranar Alhamis.
Afirka ta Kudu da Nijeriya da Ivory Coast da Laberiya da Ghana da Burkina Faso na cikin ƙasashen da suka fuskanci yankewar intanet ɗin.
Hukumar sadarwa ta Nijeriya ta tabbatar da katsewar a cikin wata sanarwa, NCC ta ce wayoyin da abin ya shafa sun taso ne daga Turai suka bi ta Gaɓar ruwan gashin Afirka.
Sun yanke ne a tekun maliya lamarin da ya shafi sauran wayoyin da ke haɗe da su a ƙarƙashin tekun.
Wasu bankuna a Nijeriya suma sun nemi afuwar abokan hulɗarsu saboda matsalar da suka fuskanta.
A Ivory Coast, ƙarfin sadarwar intanet ya ragu zuwa kashi huɗu cikin ɗari da safiyar ranar Alhamis a cewar Netblocks, kamfanin da ke bibiyar ƙarfin intanet.
No comments