Hukumar Hana Fasa Ƙauri ta Nijeriya ta dakatar da rabon kayan abinci da aka kama, sakamakon turmutsitsin da ya yi sanadin salwantar rayuka a...
Hukumar Hana Fasa Ƙauri ta Nijeriya ta dakatar da rabon kayan abinci da aka kama, sakamakon turmutsitsin da ya yi sanadin salwantar rayuka a hedikwatar hukumar na Old Zonal da ke unguwar Yaba a Jihar Legas a ranar Juma’ar da ta gabata.
Kakakin hukumar ta Kwastam Abdullahi Maiwada ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
A ranar 20 ga Fabrairu, 2024 ne Hukumar Kwastam ta ce za ta yi rabon kayayyakin abincin da aka kama domin rage wahalhalu da tsadar rayuwa ƙasar.
Da farko dai hukumar ta Kwastam ta baje kayan abinci a ofishinta na Yaba a ranar Juma’ar da ta gabata a gaban sauran jami’an tsaro kamar jami’an ’yan sandan Nijeriya.
"An fara baje kayan abincin da kyau da misalin ƙarfe 8 na safe," in ji Maiwada.
Hukumar Kwastam ta miƙa ta'aziyyarta ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan lamari. Hukumar ta bayyana cewa tana aiki tare da hukumomin kiwon lafiya don samar da tuntuɓar juna tare da yin hulɗa kai tsaye tare da dangin waɗanda abin ya shafa kan matakansu na gaba.
Bayan lamarin, hukumar ya fara bincike na ciki don fahimtar yanayin da ke tattare da abin da ya faru.
No comments