Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sayar Da Magunguna A Kasuwanni, Dole Sai Mai Ilimi A Kan Harkar -Dakta Murtala Umar

... An Taɓa Kama Wani Da Ƙwalayen Magunguna Kala-kala Yana Sanya Na Jabu A Ciji Daga Muhammad Ibrahim, Kano Ƙungiyar Masana harhaɗa magungun...

... An Taɓa Kama Wani Da Ƙwalayen Magunguna Kala-kala Yana Sanya Na Jabu A Ciji

Daga Muhammad Ibrahim, Kano

Ƙungiyar Masana harhaɗa magunguna ta ƙasa ta  bayyana cewa sayar da magani a kasuwanni da ma can haramtaccen abu ne a dokar ƙasar nan. Shugaban ƙungiyar reshen Jihar Kano, Dakta Murtala Isah Umar ne ya bayyana hakan da yake zantawa da 'yan jarida a Kano cikin makon.

Shugaban yi nuni da cewa tun a shekarun baya an yi ta ƙokari a sama wa masu sayar da magunguna cibiya tun da ba a so a ce an hana su harkar gaba ɗaya, domin abin da doka ta tanada ke nan, sayar da magani dole sai wanda yake da ilimin sanin magunguna.

Ya ce, dokar ƙasa, amma da aka ga bai kamata a hana Kasuwancin sa ba, sai aka tura mutane Indiya su kwaikwayo tsarin su.

Ya ci gaba da cewa, duk da a Indiya masu ilimin magunguna ne suke kasuwancin sa, amma a nan sai suka ce a ware wata cibiya da za a kawo jami'ai na NAFDAC da NDLEA da PSN da za su riƙa kula da shigar magunguna domin a daƙile na jabu da ake yi da miyagun ƙwayoyi da ake kawowa ana baiwa Matasa su sha su haukace.

Dakta  Murtala Isah Umar ya ce, domin haka aka ɗauki mataki na raba masu sayar da magani da kasuw, an kai su inda za a riƙa kula da hadar-hadar magunguna da suke a Ɗangwauro  domin a nesan ta su da jama'a, saboda in aka je shaguna a kasuwa ba za a  sami miyagun ƙwayoyin ba, amma idan tirela guda ake nema sai su je gida su bayar.

Daga nan sai masanin harhaɗa magunguna ya gode wa Gwamnatin Jihar Kano bisa goyon baya da haɗin kai da take baiwa ƙoƙarin tsaftace Kano daga miyagun ƙwayoyi, wanda hakan zai kawo wa mutane sauƙi daga yawaitar magunguna na jabu da kwayoyi.

Ya ce akwai wani Ibo da aka kama da matar sa akan titin Murtala Muhammad, an sami sito a gidan sa ya ajiye kwalaye da kwanson magunguna na manyan kamfani daban-daban na haɗa magunguna na jabu yana sawa yana rabawa yana sayarwa. Yanzu ana gano irin waɗannan bara gurbi ana bi su gida-gida da jami'an tsaro ana kamasu.

Dakta Murtala Isah Umar ya ce, tashin masu maganin daga kasuwa zai taimaka ya baiwa hukuma dama su tantance magungunan da ake shigowa da su Kano, ta gane masu inganci da jabu da ƙwayoyi masu illa.

No comments