Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Raɗe-raɗin Juyin Mulki: Hedikwatar Tsaro Ta Yi barazanar Gurfanar Da Kafar Sadarwa

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta yi fatali da zargin da wata kafar yaɗa labarai ta intanet ke yaɗawa kan ikirarin cewa an sanya masu tsaron fad...


Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta yi fatali da zargin da wata kafar yaɗa labarai ta intanet ke yaɗawa kan ikirarin cewa an sanya masu tsaron fadar shugaban ƙasa a shirin ko-ta-kwana bayan zarge-zargen da ake yi kan fargabar kifar da gwamnati, inda ta yi barazanar gurfanar da kafar sadarwar a kotu.

Wata sanarwa da muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron, Brigadiya Janar Tukur Gusau ya wallafa a shafinsa na X, ya ce an ankarar da su game da wani rahoto da aka wallafa a intanet a ranar 25 ga watan Fabarairun 2024 da ke ikirarin cewa masu tsaron fadar shugaban ƙasa na cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon wasu alamu da ke janyo fargabar yin juyin mulki a Nijeriya.

“Rahoton ya kuma ce zargin ya janyo yin taron gaggawa tsakanin shugaba Bola Tinubu da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa.”

Hedikwatar tsaron ta ƙaryata labarin inda ta ce an tsara masu tsaron fadar shugaban ƙasa su kare fadar da kuma babban birnin tarayya da kewayenta.

A cewar hedikwatar tsaron, a kullum jami’an tsaron da ke fadar shugaban ƙasa na cikin shiri kodayaushe domin sauke nauyin da aka rataya a wuyansu.

Hedikwatar ta kuma yi waiwaye kan yadda babban haftsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ya sha nanata ƙudurin jami’an sojin Nijeriya na kare martabar dimokraɗiyyar ƙasar.

A don haka hedikwatar tsaron ta yi kakkausar suka kan zargin inda ta buƙaci jama’a su yi watsi da shi.

Hedikwatar ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar mataki kan jaridun da ke wallafa labarin saboda mataki ne na rashin nuna kishin ƙasa.

No comments