Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tsofaffin Ɗaliban Jami'ar MAAUN Sun Ƙirƙiri Manhajar Sada Zumunta

Daga Musa Muhammad  Tsofaffin ɗaliban Jami’ar Maryam Abacha American University da ke Maraɗi a Jamhuriyar kasar Nijer sun bayyana cewa sun ƙ...


Daga Musa Muhammad 

Tsofaffin ɗaliban Jami’ar Maryam Abacha American University da ke Maraɗi a Jamhuriyar kasar Nijer sun bayyana cewa sun ƙirƙiri wata manhaja wacce al'umma za su yi amfani da ita wajen sada zumunta a tsakaninsu. 

Manhajar, wacce suka sanya wa suna da ‘Afrister’, sun ce manhaja ce da za ta kawo sauyi wajen bai wa al'umma damar ƙulla alaƙa da hulɗar zamantakewa.

Sun ƙara da cewa an tsara manhajar ta yadda za ta haɓaka hulɗa a tsakanin taitaikun mutane, iyalai, abokai, da abokan kasuwanci, wanda zai haɓaka ƙwarewar masu amfani da manhajar.

An ƙirƙiri manhajar ne a cikin shekarar 2021, a lokacin da Aliyu Ishaq da abokin aikin sa, Alhassan Abubakar suke karatunsu a Jami'ar MAAUN. 

A cewar su 'Afrister' ya sami karɓuwa cikin sauri a wurin masu amfani da shi, ganin yadda manhajar ta zo da sabbin abubuwa masu ƙayatarwa. 

A wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja, Aliyu Ishaq ya danganta nasarar Afrister da irin horon da suka samu a Jami’ar Maryam Abacha.

Ya nuna matuƙar godiyar sa ga Jami'ar sa da ya kammala, inda ya bayyana irin tasiri da ta yi masa tare da sauran ɗalibai. 

Ya kuma yaba wa wanda ya assasa Jami'ar ta MAAUN, Farfesa Adamu Gwarzo bisa irin goyon baya da jagorancin da yake bayarwa.

Domin ganin sun samu yabo da karɓuwa a duniya, Ishaq da abokin aikinsa sun ce suna aiki tuƙuru domin haɓaka Afrister, tare da tabbatar da cewa ya dace da ƙa'idodin da takwarorinsa na Yamma suka gindaya.

Ya ƙara da cewa, suna da himma da kuma ƙudurin yaɗa Afrister a duniya, wanda ya ce idan suka yi hakan, za su samu wani gagarumin ci gaba a ɓangaren masana'antar fasaha da manhajar ƙulla zamantakewa.

 

No comments