’Yan bindiga sun kashe wata budurwa mai suna Najeebah da suka yi garkuwa da ita tare da wasu ’yan uwan ta mata biyar a Abuja. An samu labari...
’Yan bindiga sun kashe wata budurwa mai suna Najeebah da suka yi garkuwa da ita tare da wasu ’yan uwan ta mata biyar a Abuja.
An samu labarin cewa an sace Najeebah da ƙannen ta ne a ranar 9 ga watan Janairu tare da mahaifinsu.
An tattaro cewa, daga baya ‘yan bindigar sun sako mahaifin nasu, inda suka nemi ya je ya biya Naira Miliyan 60 a matsayin kuɗin fansa domin a sako ’ya’yansa mata kafin ranar Juma’a 12 ga watan Janairu.
A wani yunƙuri na neman kuɗi, an buƙaci tallafi daga ‘yan Nijeriya da su ba da gudunmawar duk abin da ya sawwaƙa a zuwa wanu asusun banki, amma har zuwa ranar Juma’a ba a tara isassun kuɗaɗe ba.
Sakamakon haka, ‘yan bindigar sun kashe babbar budurwa a cikin ‘yan matan shida mai suna Najeebah, inda suka jefar da gawarta a wani wuri domin iyayenta su binne.
Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Digital, Isa Ali Pantami, ya tabbatar da kashe Najeebah a daren Asabar.
Pantami ya ce ya tattauna da mahaifin Najeebah kan sauran ‘yan matan da aka sace.
“Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raajiun! Na samu labarin kashe ɗiyar mu Najeeba. Na kuma yi magana da mahaifinta game da ragowar ’ya’yanmu mata 5 da aka sace. Allah ya gafarta mata, ya kubutar da sauran, ya kawo mana cikakken zaman lafiya a Nijeriya,” inji shi a wani sakon da ya wallafa a shafin sa na X.
Tun da farko, wani tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya bukaci ‘yan sanda da su ɗauki matakin da ya dace kan lamarin.
No comments