Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Dakta Idris Dutsen Tanshi

Wata kotun Shari'ar Musulunci a Jihar Bauchi da ta mayar wa da waÉ—anda suka tsaya wa Dakta Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi takardun k...



Wata kotun Shari'ar Musulunci a Jihar Bauchi da ta mayar wa da waɗanda suka tsaya wa Dakta Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi takardun kadarorinsu da suka bayar domin karɓar belin shi da ta bayar a baya.

Wannan mataki dai na nufin kotun ta janye belin da ta bayar kan Dakta Idris, wanda kuma hakan yake nufi za a iya kama shi.

Barista Ahmad Musa Umar shi ne lauyan da ke kare Dr Idris, ya ce "kotu za ta iya bai wa 'yan sanda takardar kama Dakta Idris a kowanne lokaci".

"Kotun ta ce ta É—age shari'ar zuwa ranar 24 ga watan nan na Janairu, wanda kuma take tsammanin jami'an tsaro sukai mata shi gabanin wannan rana," inji Barista Ahmad Musa.

Ana dai tuhumar Dakta Idris ne da laifuka biyu, na farko kalaman ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.W.

Na biyu kuma ana tuhumarsa da laifin tayar da zaune tsaye.

Har yanzu dai ba a fara sauraran wannan shari'a ba kan waÉ—annan tuhume-tuhume.

No comments