Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zargin Haƙar Ma'adanai Ba Bisa Ƙa'ida Ba: NUMW Ta Nisanta Kan Ta

Daga Muhammad Awwal a Minna Tun bayan da gwamnatin jihar Neja ta shelanta dakatar da haƙar ma'adanan ƙasa a jihar, Ƙungiyar leburori mas...

Daga Muhammad Awwal a Minna

Tun bayan da gwamnatin jihar Neja ta shelanta dakatar da haƙar ma'adanan ƙasa a jihar, Ƙungiyar leburori masu aikin haƙar ma'adanan, reshen jihar Neja, bisa jagorancin Kwamared Musa Adamu Nasko ta tabbatar da goyon bayanta ga dokar ta gwamnati bisa dalilan tsaro, ta kuma nisanta kan ta game da waɗanda suka karya dokar. 

Ƙungiyar ta ce, har yanzu suna kan bakar su wajen goyon bayan gwamnati akan wannan ƙuduri, duk da cewar dukkanin ƙa'idojin da gwamnatin ta sharɗanta sun cika su, amma ba za su koma bakin aikin ba sai tare da umurninta.

Kan haka Matattarar Labarai ta ziyarci Ƙaramar Hukumar Paikoro, inda aka samu rahoton wasu na ci gaba da aikin haƙar ma'adanan har yanzu.

Malam Mustapha Abdullahi, shi ne shugaban Ƙungiyar masu haƙar ma'adanan ta NUMW, reshen Karamar Hukumar Paikoro, ya bayyana cewar, "mu kan mu mun samu labarin cewa zuwa yanzu wasu na ci gaba da aikin, amma tun da uwar Ƙungiya ta jiha, bisa jagorancin Musa Nasko ta umurce mu da dakatawa, muka sanar da 'ya'yan ƙungiya, kuma tsawon lokacin nan ba mu koma fagen aiki ba.

"Duk wani da ka ga yana aikin nan a Ƙaramar Hukumar Paikoro, to ba ɗan ƙungiyar mu ba ne. Don gudun ɓatanci, mun sanar da uwar ƙungiya ta jiha halin da ake ciki, kuma ta ba mu shawarwarin hanyoyin da za mu bi, wanda yanzu haka akan su muke.

"Muna da rahoton wuraren da ake ci gaba da aikin, kuma jami'an tsaro har sun kai ga kama mutane uku, yanzu haka suna gaban Ƙuliya, amma ba 'ya'yan ƙungiyar mu ba ne. Don haka muna ƙara jaddada goyon bayan mu ga uwar ƙungiya ta jiha bisa bin umurnin gwamnatin jiha."

Malam Abubakar Musa, wanda shi ne ma'ajin ƙungiyar a Ƙaramar Hukumar Paikoro, ya ce, "muna kira ga gwamnatin jiha, da ta tausaya mana, domin ba mu da wata hanyar cin abinci face wannan, kuma yanzu tsawon lokaci muna zaune, ya kamata waɗanda abin ya shafa da su baiwa Maigirma Gwamna shawara da a ɗage wannan dokar don samun ci gaba. 

"Da yawan mu suna da iyali, kuma ba wani tallafin da muke samu daga gwamnati, tun daga lokacin da uwar ƙungiya ta umurci da mu janye daga bakin aikin bisa umurnin gwamnati, muka janye. Shi ya sa lokacin da rahoton ya zo mana cewar wasu sun koma bakin aikin muka yi gaggawar kiran 'ya'yan ƙungiya da suka yi rajista da 'Nigeria Union of Mine Workers' da su tabbatar sun bi umurnin gwamnati kamar yadda uwar ƙungiya ta jiha ta umurce mu."

Makilin Matattarar Labarai ya binciko cewar jami'an tsaro na ci gaba da yin rangadi, tare da cafke mutane da dama bisa laifin take dokar gwamnatin jiha na hana ci gaba da haƙar ma'adanan.

 

No comments