Aƙalla mutane shida ne suka mutu yayin da wasu 50 ke kwance a asibitin Jukun da ke Ƙaramar Hukumar Karim-Lamido a Jihar Taraba sakamakon ɓar...
Aƙalla mutane shida ne suka mutu yayin da wasu 50 ke kwance a asibitin Jukun da ke Ƙaramar Hukumar Karim-Lamido a Jihar Taraba sakamakon ɓarkewar cutar amai da gudawa.
Ɓarkewar, a cewar mazauna yankin ta fara ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata lokacin da mutanen yankin musamman ƙananan yara suka fara mutuwa.
Kwamishinar lafiya na jihar Taraba, Bodiya Buma, ta tabbatar da faruwar lamarin yayin da aka tuntuɓe ta. Ta ce gwamnatin jihar ta san da faruwar lamarin kuma tana baƙin ƙoƙarinta wajen shawo kan lamarin.
Daraktan kula da lafiya a matakin farko na ƙaramar hukumar Karim Lamido, Mista Fredrick Nyanganji, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, ya ce annobar ta faro ne a ranar 14 ga watan Disamba, 2023.
“Mun samu rahoton cewa ruwa yana ƙarew manya da ƙananan yara a cikin a sanadiyyar matsananciyar amai da ake zargin kwalara ce,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho.
Mataimakin shugaban karamar hukumar, Alhaji Musa Karim wanda ya jagoranci wata tawaga zuwa ga al’ummar da abin ya shafa a madadin shugaban zartaswar Karim Lamido, Mista Bitrus Dan Jos, ya shaida wa wannan jarida cewa kimanin yara da manya 30 ne aka kwantar da su a ranar Alhamis din da ta gabata. Ma’aikatar lafiya matakin farko a yankin da Yara shida sun mutu a cikin wannan annoba.
No comments