A halin yanzu dai dubun wasu ’yan sanda biyar ya cika, sakamakon kama su da aka yi suna rakiya, tare da bayar da kariya ga dillalan miyagun ...
A halin yanzu dai dubun wasu ’yan sanda biyar ya cika, sakamakon kama su da aka yi suna rakiya, tare da bayar da kariya ga dillalan miyagun ƙwayoyi wajen yin safarar hodar Iblis.
Dubun ’yan sandan da ake tsare a halin yanzu ta cika ne a lokacin da suke rakiyar dilar hodar Iblis mai tarin yawa a jihar Legas.
Waɗanda aka kama ɗin suna aiki ne a runduna ta musamman ta shugaban ’yan sanda kan yaƙi da muggan laifuka.
An kama su ne bayan musayar wuta da ’yan sandan farin kaya da suka samu labarin mugun aikin, suka kuma yi ƙoƙarin kama dillalan ƙwayoyin a yankin Vicoria Island.
Wani babban ɗan sanda ya bayyana cikin sirri, cewa bayan an tsayar da waɗanda ake zargin domin bincike sai suka fara barazana ga jami’anmu suna harbi a iska.
“Amma duk da haka, jami’anmu suka ƙi janyewa su bar su su wuce, da aka bincika kuma sai aka kama su da tulin miyagun ƙwayoyi, waɗanda bayanai suka nuna hodar iblis ce.
Jami’in ya ci gaba da cewa, “ana cikin haka sai jami’an NDLEA suka iso wurin, amma da suka nemi su tafi da ƙwayoyin sai waɗancan suka ci gaba da harbe-harbe, suna neman hana su.
“Hakan ne ya sa sojoji suka iso wurin, suka tafi da ƙwayoyin barikinsu da ke Bonny Camp, daga nan Kwamandan su ya kira AIG mai kula da Zone 2, aka zo aka tafi da ita.”
Waɗanda aka kaman, sun haɗa da waniai muƙamin DSP, Fayomi Abraham, ASP Emmanuel Bentong, Inspector Salami Femi, Inspector Ashimi Adedokun da Sajan Alex Akeredolu.
No comments