Daga Imrana Abdullahi A ƙoƙarin ganin sun ciyar da Jami'ar Bayero da ke Kano gaba, a ranar 16 ga watan Disambar nan na 2023 ne ƙungiyar ...
Daga Imrana Abdullahi
A ƙoƙarin ganin sun ciyar da Jami'ar Bayero da ke Kano gaba, a ranar 16 ga watan Disambar nan na 2023 ne ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Jami'ar suka zaɓi sababbin shugabannin da za su tafiyar da ƙungiyar.
Ƙungiyar ta 'BUK Alumni Association BUKAA' ta zaɓi sababbin shugabannin n, inda aka zaɓi Alhaji Shu'aibu Idris Miƙati a matsayin shugaba na ƙasa, wanda ya guda a harabar makarantar da ke Kano.
Waɗanda aka zaɓa ɗin su ne;
1. Shugaba - Alhaji Shuaibu Idris Miƙati
2. Mataimakin shugaba na I - Aare Akinwumi Akinyemi
3. Mataimakin shugaba na II - Ahmed Abdulƙadir Firdaus
4. Sakatare Janar- Alhaji Salisu Indabawa
5. Mataimakin Janar Sakatare na I - Ma'aruf Zakariya
6. Mataimakin Janar Sakatare na II -Mairo D Suleiman
7. Sakataren kuɗi - Safiya Stephanie Musa
8. Mai binciken kuɗi - Amb. Adamu Babangida
9. Ma'ajin Ƙungiya - Lawal Ali Gujungu
10. Mai kula da jin daɗi da walwala - Mustapha A. Dawaki
11. Mai bayar da shawara a kan harkokin shari'a - Barr. Saidu Tudunwada
12. Sakataren yaɗa labarai - Mukhtar Zubairu Surajo
13. Dr. Bala Muhammad – Wakilin Ƙungiya daga yankin Arewa maso Yamma.
14. Alhaji Ibrahim Idris Danisan Fika - Wakilin ƙungiyar daga yankin Arewa maso Gabas
15. Aliyu Emu Yusuf - Wakilin ƙungiyar daga yankin Arewa ta tsakiya.
16. Joseph Adewale Rannaiye - Wakilin kungiyar daga yankin Kudu maso Yamma
17. Olorogun Oyibo Adejero Mohammed - Wakilin ƙungiyar daga yankin Kudu maso Kudu.
18. Lawrence Juwah - Wakilin ƙungiyar daga yankin Kudu maso Gabas.
No comments