Alƙalin-Alƙalan jihar Neja, Mai Shari'a Halima Ibrahim Abdulmalik ta karanta hukuncin kisa ta hanyar ratayewa da aka yanke wa wani mat...
Alƙalin-Alƙalan jihar Neja, Mai Shari'a Halima Ibrahim Abdulmalik ta karanta hukuncin kisa ta hanyar ratayewa da aka yanke wa wani matashi mai suna Stephen Jiya, bisa kama shi da laifin yi wa mahaifiyar sa, Mrs Comfort Jiya, mummumar kisan gilla ta hanyar ƙonewa. Mai Shari'ar ta miƙa yanke wannan hukunci ne a babbar kotun jihar ta 1 da ke Mina.
Marigayiyar, wacce ta kasance tsohuwar shugabar makarantar mata ta gwamnati da ke Sabon Wuse da kuma Kwalejin kimiyya ta Maryam Babangida da ke Mina ce, ta gamu da ajalin ta ne yayin da wannan ɗa na ta, ya banka mata wuta a kicin ɗin da ke gidan ta da ke yankin Darussalam a Mina, wanda kuma a ka tabbatar ya na shaye-shaye.
Yayin da maƙwabta suka ga abin da ke faruwa ne, sai suka garzaya da Comfort zuwa babban asibitin gwamnati da ke Mina, wanda kuma daga bisani aka canja mata wani asibitin, inda a nan ne ta rasu sakamakon ƙunar da ta samu.
Jami'an tsaro na sashen binciken sirri na rundunar 'yan sanda ta SCID ne suka cafke mai laifin, wanda kuma aka tuhuma a ƙarƙashin doka ta 221ta Final Kot, wanda kuma a nan ne aka samu hukuncin kisa kan mai laifin.
Tun a ranar 22 ga watan Nuwambar 2022 ne aka fara sauraren wannan ƙara, wanda kuma Mai Shari'a Halima Abdulmalik ta karanta hukuncin a ranar 13 ga wannan wata na Disambar 2023.
Mai Shari'a Halima Abdulmalik ta ce duk wani bincike da ya kakata a yi, an yi, inda aka samu mai laifin da hannu dumu-dumu a laifin da ya aikata, wanda kan hakan ne ta kai ma yanke masa wannan hukunci na kisa.
Ta ci gaba sa bayyna cewa, mai gabatar da ƙara ya bayar da hujjojin da ke tabbatar da cewa Stephen Jiya ya aika laifin da ake tuhumar sa a kai, don haka bisa doka ya cancanci wannan hukunci da aka yanke masa.
Kafin ta karanta hukuncin na ƙarshe, Mai Shari'a Halima ta tambayi wanda ake tuhuma kan cewa ko ya na da abin cewa, kafin ta zartar da hukuncin.
Mai laifin ya roƙi kotun da ta yi masa rangwame. Ya ce, "Ina da iyali, ina da mata da 'ya'ya. A ba ni wata damar, zan zama mutumin kirki ga al'umma. Ki tausaya mani, ki yi mani adalci. Na yi alƙawari zan canja halaye na zuwa nagari."
Lokacin da ta ke karanta hukuncin, wanda ta kwashe fiye da awa ɗaya tana karantawa, Mai Shari'a Halima Abdulmalik ta bayyana cewa ba za ta iya yin komai ba, domin hukuncin wanda ya aikata kisa, shi ne a kashe shi.
Ta ce, "A wannan yanayin, hukuncin kotu a kan ka, shi ne a rataye ka a wuya, ko a jona maka wayar lantarki har sai ka mutu, ko kuma a yi maka allurar mutuwa. Allah ya ji ƙan ka."
Mutane shida ne suka bayar da shaida a kan sa a gaban kotun, ciki har da ƙanuwar sa, da wasu mutum biyu daga cikin dangin sa.
No comments