Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Samu Ɓarkewar Zazzaɓin Dengue A Sakkwato, Wacce Ta Fi Zazzaɓin Cizon Sauro

Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa a Nijeriya, NCDC ta tabbatar da ɓarkewar cutar zazzaɓin Dengue a Jihar Sakkwato da ke Arewacin Nijeriy...



Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa a Nijeriya, NCDC ta tabbatar da ɓarkewar cutar zazzaɓin Dengue a Jihar Sakkwato da ke Arewacin Nijeriya, wacce aka ce ta fi zazzaɓin cizon sauro lahani.

Babban Daraktan hukumar ta NCDC, Dakta Ifedayo Adetifa wanda ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja, ya ce mutum 71 ake zargin sun kamu da cutar, an tabbatar da mutum 13 ne sun kamu, sai dai babu rahoton asarar rai daga ƙananan hukumomin jihar uku da aka samu ɓullar cutar.

Adetifa ya bayyana cewa galibin mutanen da ake zargin sun kamu da cutar ’yan shekara tsakanin 21 da kuma 40 ne inda ya ce an gano hakan cikin watan Nuwambar 2023.

Babban daraktan hukumar ya ce ɓarkewar cutar a yanzu yana mataki na matsakaici la'akari da binciken da aka yi game da haɗarin cutar. Ya kuma ce akwai isassun kayan aiki da kuma ma'aikatan lafiyar da za su duƙufa ko da an samu ɓarkewar cutar a sauran jihohin ƙasar.

Zazzaɓin Dengue cuta ce da sauro ke yaɗa ta a yankuna masu zafi da wuraren da ke maƙwabtaka da su.

Alamominta sun hada da zazzabi da ciwon kai da tashin zuciya da amai da ciwon gaɓɓai, da fitowar ƙurji. A wasu lokuta kuma, tana iya janyo mutuwa.

Ɓarkewar dengue a Nijeriya wani ɓangare ne na ɓullar cutar a watannin baya-bayan nan a wasu ƙasashen Afirka kamar Senegal da Burkina Faso da Cabo Verde da Chadi da Ethiopia da Mali da Togo.

A cewar wata ƙididdiga daga hukumar kare cututtuka masu yaɗuwa ta Afirka, Burkina Faso ce ƙasar da cutar ta fi ƙamari inda aka samu mutum fiye da 600.

No comments