Sojojin da suka karɓi mulki a Jamhuriyar ƙasar Nijar sun amimce da sharuɗɗan miƙa mulki ga gwamnatin Farar Hula, kuma za su gabatar da tsari...
Sojojin da suka karɓi mulki a Jamhuriyar ƙasar Nijar sun amimce da sharuɗɗan miƙa mulki ga gwamnatin Farar Hula, kuma za su gabatar da tsarinsu na yin haka ga ƙungiyar ECOWAS, a cewar wani jam’in Diflomasiyyar ƙasar Tog, wacce ke shiga tsakanin ɓangarorin biyu.
Ministan Harkokin Wajen Tog, Robert Dussey ne ya bayyana haka ranar Alhamis a wata hira da gidan talbijin na Jamhuriyar Nijar.
Ya ce an cimma yarjejeniya game da lokaci da kuma tsare-tsaren miƙa mulki, a ganawarsu da Firaiministan Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine da Ministan harkokin waje, Bakary Yaou Sangare.
“Mun shirya gabatar da tsare-tsare ga shugabannin ƙasashen da ke shiga tsakani da kuma Majalisar ECOWAS,” in ji shi.
ECOWAS ta sanya wa Nijar jerin takunkumai, ciki har da na rufe kan iyakokin mambobinta da katse lantarki da ake ba ta daga Nijeriya da kuma dakatar da ƙasar daga harkokin kuɗi na ƙungiyar, tun da aka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
Bincike ya nuna cewa waɗannan takunkuman da aka sanya wa Nijar da kuma cire ta daga cikin harkokin ƙasashen duniya sun jefa ta cikin ƙarin matsin tattalin arziki.
A watan Oktoban da ya gabata, shugabannin sojojin sun sanar da rage kashi 40 cikin ɗari na kasafin kuɗin ƙasar na 2023 sakamakon takunkuman da ƙasashen duniya da na lardi suka sanya mana.
A taron ECOWAS na ranar Lahadin makon jiya, shugabanninta sun gindaya wa sojojin Nijar sharuɗɗa kafin su cire musu takunkuman.
Sun naɗa kwamitin mutum uku na shugabannin ƙasashen Togo da Benin da Saliyo domin tattaunawa da sojojin Nijar da kuma bibiyar yadda za su cika waɗannan sharuɗɗan.
A baya dai, sojojin na Nijar sun ce za su iya kwashe shekara uku a kan mulki kafin su sauka.
No comments