Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Bindiga Sun Ƙona Mace Da 'Ya'yanta Biyu A Sakkwato

Wasu ’yan ta'adda da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun ƙona wata uwa da surikarta da ’ya’yanta biyu a wani hari da suka kai a jihar...



Wasu ’yan ta'adda da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun ƙona wata uwa da surikarta da ’ya’yanta biyu a wani hari da suka kai a jihar Sakkwato. 

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun kai hari ne ƙauyen Kurya da ke Ƙaramar Hukumar  Raɓah ta jihar Sakkwato da misalin ƙarfe 8:30 na daren Lahadi.

Rahotannin sun ce, 'yan ta'addan sun kashe mutanen ƙauyen 12 tare da sace mata 3 yayin harin.

Wani mazaunin yankin, Yusuf Garba ya ce ɗaya daga cikin waɗanda aka sace ta rasa mijinta a harin.

"Daga cikin waɗanda aka kashe akwai wata mace ɗaya da aka ƙona ta mutu tare da surukarta da 'ya'yanta biyu a cikin ɗakinsu," inji shi.

A cewarsa, daga baya maharan sun yi wani ƙazamin faɗa da sojoji.

“Muna zargin su ma sun yi asara mai yawa saboda mun ga tabon jini a inda suka ajiye babura. Amma ka san ba sa barin gawarwakinsu,” inji shi.

Sai dai rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai yayin harin.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmed Rufa’i, ya kara da cewa suna cigaba da tattara alkaluman waɗanda suka mutu.

Idan dai za a iya tunawa, a tsakanin ranar Alhamis da Asabar din da ta gabata, sojoji sun kuɓutar da mutane 66 da aka yi garkuwa da su, bayan sun kai farmaki dajin Gundumi da ke gabacin jihar.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa wannan jarida cewa an kashe ‘yan fashi da dama a yayin farmakin.

No comments