Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NDLEA Ta Cafke ’Yar Shekara 75 Bisa Laifin Safarar Miyagun Ƙwayoyi

Hukumar Yaƙi da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA ta bayyana cewa, an kama wata kaka mai shekaru 75 a Legas da laifin safarar m...



Hukumar Yaƙi da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA ta bayyana cewa, an kama wata kaka mai shekaru 75 a Legas da laifin safarar miyagun ƙwayoyi.

An kama wadda ake zargin mai suna Sekinat Soremekun ne a ranar Juma’a a unguwar Oshodi da ke Legas tare da kwato tabar wiwi da litar maganin codeine daga hannunta.

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya ce kakan ta yi ikirarin cewa ɗanta mai suna Segun wanda a halin yanzu yake hannunta, ya kawo mata haramtattun kayan da ta sayar.

"Jami'an NDLEA a Legas a ranar Juma'a 15 ga watan Disamba sun kama wata kaka mai shekaru 75, Sekinat Soremekun da laifin safarar miyagun ƙwayoyi," inji Babafemi a cikin wata sanarwa.

Hakazalika hukumar ta yi nasarar gano wani katafaren gida na miliyoyin naira da ke kan titin K-5A/2 Road 14, Victoria Garden City (VGC) estate, unguwar Lekki da ke Legas da aka yi amfani da shi a matsayin dakin gwaje-gwaje na ɓoye ƙwayar methamphetamine.

No comments