Wasu ’yan bindiga sun kashe wani mutum a ƙauyen Kwalfada da ke cikin Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara saboda ya hana ’yarsa auren ɗan f...
Wasu ’yan bindiga sun kashe wani mutum a ƙauyen Kwalfada da ke cikin Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara saboda ya hana ’yarsa auren ɗan fashi.
Wani ɗan ƙauyen mai suna Mallam Rabo ya shaida wa manema labarai cewa ɗaya daga cikin ‘yan fashin ya nemi auren ɗaya daga cikin ‘yan matan ƙauyen amma mahaifinta ya ƙi amincewa.
Mahaifin, a cewar Rabo, ya yanke shawarar bai wa faya daga cikin mutanen ƙauyen auren ‘yarsa a maimakon ɗan fashin.
Rabo ya ce, “Bayan an daura auren ne sai ‘yan bindigar suka mamaye yankij inda suka kashe mahaifin yarinyar.
“Sun kuma buƙaci mijin yarinyar ya sake ta domin abokin aikinsu ya aure ta.
“Sun yi barazanar kashe mijin idan bai bi umarnin ba.
"Nan da nan mijin ya saki matar kuma ta sake yin aure ga ɗan fashin da ya kai ta daji."
Rabo ya koka da cewa ‘yan fashin sun daɗe suna ta’addanci ga al’umma kuma babu wani mataki da hukumomi suka ɗauka na samar da tsaro ga mazauna garin.
Ya ce, ‘yan fashin sun forawa ƙauyen harajin Naira Miliyan huɗu makonnin da suka gabata.
No comments