Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Lawal Ya Rantsar Da Kantomomin Ƙananan Hukumomin Jihar 14

  Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, a bikin rantsar da Kantomomin da za su kula da Ƙananan Hukumomin jihar 14, ya jawo hankalin su wajen a...

 

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, a bikin rantsar da Kantomomin da za su kula da Ƙananan Hukumomin jihar 14, ya jawo hankalin su wajen aiwatar da ayyuka don samun masarar manufofin gwamnati. 

An gudanar da bikin rantsarwar ne a Sakatariyar ma'aikatan jihar ta J. B Yakubu Secretariat da ke Gusau a yau Alhamis ɗin nan, kamar yadda ya ke ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu. 

Sanarwar ta ce, Gwamna Lawal ya kuma hori Sabbin Kantomomin kan su jajirce wajen aiki tuƙuru don su tabbatar da tsammanin da ake masu wajen zaɓo su. 

Ya ce, an kuma hore su da su yi aiki tuƙuru wajen aiwatar da manufofin gwamnati na inganta rayuwar al'ummar jihar, musamman a fannonin samar da tsaro da samar da ababen more rayuwa. 

Gwamna Lawal ya bayyana wa Ƙantomomin cewa cancanta, jajircewa da ƙwarewa a aiki ne suka sa aka zaɓo su don wannan aiki, wanda waɗannan alamomi ne suka sa aka damƙa masu jagorancin Ƙananan Hukumomin don kula da su kafin Hukumar zaɓe ta jiha ta kammala shirye-shiryen ta na gudanar zaɓen Ƙananan Hukumomin jihar. 

Sanarwar ta Sulaiman Bala, ta kuma bayyana cewa an zaɓo waɗannan shugabanni ne don jagorancin Ƙananan Hukumomin bisa la'akari da gaskiyar su, mutuncin su da kuma irin gudumawar da kowannen su ya bayar wajen ci gaban al'ummar sa, tare da irin goyon bayan da suka bayar wajen tsamo jihar Zamfara daga mawiyacin halin da ta ke ciki. 

“Kyakkyawan shirin da za ku yi don fuskantar wannan nauyi da aka ɗora maku, shi ne mafi a'ala, musamman bisa la'akari da cewa Ƙananan Hukumomi ne mataki na uku a gwamnatance, sannan su suka fi kusa da jama'a" in ji Gwamna Lawal. 

Don haka ya hore su da su samar da abokan aiki nagari, sannan su yi aiki tare da Sakatarorin Ƙananan Hukumomin da Kansiloli. 

Bayan da aka kammala jawabai ne, sai Gwamna Lawal ya mimmiƙa masu takardun kama aiki, inda za su yi aiki na tsawon watanni shida

No comments