Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ba Mu Janye Ko Rage Kuɗaɗen Da Ke Yawo A Tsakanin Jama'a Ba -CBN

  Babban bankin Nijeriya (CBN) ya sake tabbatar wa al'ummar ƙasar nan cewar akwai isassun takardun kuɗi na Naira tare da kwantar da han...

 

Babban bankin Nijeriya (CBN) ya sake tabbatar wa al'ummar ƙasar nan cewar akwai isassun takardun kuɗi na Naira tare da kwantar da hankalin mutane na daina shiga firgici saboda ƙarancin kuɗaɗe a bankuna.


Babban bankin, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ta hannun Kakakin sa, Isah Abdulmumin, ya sake nanata cewa tsofaffi da sabbin takardun kuɗi na Naira suna daram.



“Don kaucewa shakku, muna nanata cewa akwai isassun takardun kuɗi a faɗin ƙasar nan don gudanar da duk harkokin tattalin arziki na yau da kullum,” in ji kakakin CBN, Isa AbdulMumin.


“Saboda haka, an umarci rassan bankin CBN a faɗin ƙasar nan da su ci gaba da fitar da takardun kuɗi daban-daban na tsofaffi da sabbi cikin adadi mai yawa zuwa bankunan kasuwanci don ci gaba da rarrabawa ga abokan huldar bankuna.


“Muna so mu sake bayyana cewa duk takardun kuɗi na banki da CBN ke bayarwa suna nan a kan doka. Kamar yadda sashe na 20 (5) na dokar CBN ta shekarar 2007, babu wanda ya isa ya ƙi karɓar Naira a matsayin hanyar biyan kuɗi.”


 

CBN “ya sake tabbatar da cewa akwai isassun takardun kuɗi don sauƙaƙa ayyukan tattalin arziki na yau da kullum”.


In dai za iya tunawa, watan Oktobar shekarar da ta gabata ne tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana shirin sake fasalin wasu kuɗaɗe, sannan ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su musanya tsofaffin takardunsu kafin ranar 31 ga watan Junairu, 2023.


Wannan hukunci ya haifar da taɓarɓarewar tattalin arziki yayin da ‘yan Nijeriya da dama suka shiga mawuyacin hali, lamarin da ya haifar da tarzoma a wasu jihohin da kone wasu bankuna da kuma injinan cire kuɗi.


Daga baya bankin ya amince da tsawaita wa’adin canjin takardun Naira.


Wasu gwamnonin jam’iyyar APC na wancan lokacin sun kai CBN da gwamnatin tarayya zuwa kotun ƙoli inda kotun ta yanke hukunci a watan Maris na 2023 cewa tsofaffin takardun kuɗi na N200, N500, da N1,000 za su ci gaba da aiki har zuwa ranar 31 ga Disamba. , 2023.


No comments