Daga Ibrahim Muhammad, Kano Kwamiti mai tuntubar ƙungiyoyin ƙwararru, masana da ƙungiyoyin ƙwadago, domin tallata buƙatar Gwamnan Jihar Kano...
Kwamiti mai tuntubar ƙungiyoyin ƙwararru, masana da ƙungiyoyin ƙwadago, domin tallata buƙatar Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na neman goyon baya da gudumawa domin samun nasara a zabe mai zuwa na 2027, ya ziyarci wasu ƙungiyoyi a Kano.
Ƙarƙashin jagorancin Daraktan Kwamitin na Jihar Kano, Kwamared Inusa Isah Danguguwa, tawagar da ta ƙunshi mambobin kwamitin guda 8, ta kai ziyarar ne a yammacin ranar Litinin, zuwa hedikwatar sakatariyar Kungiyar Malaman Makaranta (NUT) ta Jihar Kano, da sakatariyar Kungiyar Ma'aikatan Kananan Hukumomi (NULGE), da sakatariyar Kungiyar Likitoci (NMA) ta Jihar Kano, inda ƙungiyoyin suka yi musu kyakkyawar tarba.
A jawabinsa a lokacin da suka je sakatariyar NUT na Jihar Kano, Daraktan Kwamitin, Kwamared Inusa Isah Danguguwa, ya bayyana cewa sun zo ne domin neman goyon bayan Kungiyar Malaman Makarantu, su bai wa Gwamnan Jihar Kano da Jam'iyyar APC goyon baya domin samun nasara a zabe mai zuwa.
Ya bayyana irin ɗimbin ayyukan alkhairi na kyautatawa da bunƙasa ci gaban Malamai da ilimi da Gwamna Abba Kabir ya gudanar, waɗanda suka haɗa da biyan albashi a kan lokaci, da karin girma da ake yi wa malamai, da kuma samar da yanayi mai inganci na gudanar da koyarwa a makarantu.
A jawabinsa, Shugaban NUT na Jihar, Kwamared Baffa Ibrahim Garko, ya bayyana gamsuwa da irin kyautatawa da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi wa malamai, kuma suna yi masa godiya a kai, duba da irin kyautatawa da yake musu, tun daga kan biyan albashi a kan lokaci, da karin girma, wanda har zuwa yanzu ba su da matsalar promotion ko daya.
Ya ce an samar da kayan koyo da koyarwa, ana kuma ba da horo akai-akai ga malaman makaranta a fannoni daban-daban na kyautata jin dadinsu da aikinsu. Dan haka ba abin da za su ce wa Gwamna sai godiya.
Ya ce a wannan tafiya, suna yi wa kwamitin alkawarin cewa sun karbe ta, za su yi aiki tuƙuru domin ganin samun nasarar Gwamna, saboda an riga an kyautata musu, su ake jira su biya bashi, da yardar Allah za su biya, saboda samun nasarar Gwamna a 2027 ba tasa ba ce shi kaɗai, nasara ce ta al'ummar Kano.
Ya ce za su ƙara ƙoƙari domin habaka harkar koyo da koyarwa, su ga cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ga nasara, kuma wannan goyon bayan da ake nema, malaman makaranta sun karba, kuma da yardar Allah za su saka da alheri.
Baffa Ibrahim Garko ya mika rokon NUT ga kwamitin, a kan ya isar da sakonsu ga Gwamna, na neman a daidaita musu albashin Jiha da na Kananan Hukumomi. Idan aka yi musu wannan, malami musamman na firamare, ba shi da wata matsala, ya'yansa da duk wanda yake tare da su, Gwamna Abba za su zaba.
A lokacin da kwamitin ya ziyarci shugabannin Ƙungiyar Ma'aikatan Ƙananan Hukumomi, Kwamared Inusa Isah Danguguwa ya bayyana irin ayyukan da Gwamnan Kano ya gudanar na kyautatawa ma'aikatan kananan hukumomi, tare da kira a gare su, su bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf karin goyon baya domin samun nasarar Jam'iyyar APC a zaben 2027.
Shi ma a jawabinsa, Shugaban NULGE na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Muhammad, ya bayyana jin dadinsa da ziyarar tawagar, tare da bayyana irin kyautatawa da Gwamnan Kano ya yi wa 'ya'yan kungiyar, ta tura ma'aikatan kananan hukumomi na kowane sashi bita. A wannan tsari, a nan gaba har ƙananan ma'aikata da masinjoji za a tura, sannan ga kyautar kujerun Hajji da ake bai wa mambobinsu. Dan haka a shirye suke, za su ba da goyon baya don ganin nasarar Gwamna a karo na biyu.
A ziyarar da kwamitin ya kai ga sakatariyar Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa, "National Medical Association (NMA)", reshen Jihar Kano, Shugaban Kwamitin, Kwamared Inusa Danguguwa, ya bayyana cewa sun zo ziyarar neman goyon bayansu ne, domin samun nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf, musamman idan aka yi la'akari da irin muhimman ayyuka da aka gudanar a fannoni daban-daban na inganta lafiya.
Da yake jawabi, Shugaban Kungiyar ta NMA, Dakta Abubakar Nagoma, ya bayyana cewa a shirye kungiyar take ta bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf goyon baya, saboda irin ayyukan da ake yi na kyautata harkokin lafiya.
Da yake ƙarin bayani a kan maƙasudin ziyarar ga 'yan jarida, Daraktan Kwamitin, Kwamared Inusa Isah Danguguwa, ya ce wannan ziyara da suka kai wa NUT, NULGE da NMA, ziyara ce ta kawo musu sakon Gwamnan Jihar Kano da kuma Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na neman goyon baya da gudummuwa da taimakon kungiyoyin, domin idan an zo zaben 2027, Allah ya ba su nasarar Gwamna da Shugaban Kasa su maimaita a kan kujerun su.
Ya ce dukkanin ƙungiyoyin, kowanne ya bayyana ayyukan alkhairi da suka ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, sun yi, kuma sun gabatar musu da wasu buƙatu da shawarwari da suke ganin akwai bukatar Gwamna da Shugaban Ƙasa su ɗauki mataki a kai, don ƙara kyautata abubuwan da ake yi na alkhairi, al'ummar Kano da na ƙasa su ci gaba da cin moriyar Dimokuraɗiyya.
Danguguwa ya ce ziyarar ta kara musu kwarin gwiwa, domin wadanda suka ziyarta, su suke ambata musu ayyukan alheri da Gwamna Abba Kabir ya yi, duk da ƙalubale da dama da ya riƙa fuskanta a cikin waɗannan shekaru uku, amma ya yi abin da ya cancanta.
Dukkanin ƙungiyoyin nan sun amince za su ba da gudummuwa domin zabar Gwamna, ya ci gaba da ba da gudumawa wajen kyautata ci gaban al'umma.

No comments