Daga Zubairu Lawal, Lafia Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), Seyi Makinde, ya ce z...
Daga Zubairu Lawal, Lafia
Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), Seyi Makinde, ya ce zai iya sake tsara Najeriya cikin shekaru huɗu idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a shekarar 2027.
Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin taron tattaunawa na APM na shiyyar Arewa ta Tsakiya, wanda aka gudanar a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, inda ya gode wa Gwamna Abdullahi Sule da al’ummar jihar bisa karɓar bakuncin tawagarsa.
Da yake jawabi ga magoya bayansa da suka haɗa da mata masu aikin noma, ’yan kasuwar mata, mata masu nakasa da zawarawa, Makinde ya ce saƙonsa shi ne, “idan ruwa ya yi yawa, dukkan kwale-kwale za su tashi.”
Ya ce gwamnatinsa za ta samar da shirye-shirye na musamman domin tallafa wa ƙungiyoyin marasa ƙarfi, tare da sake tsara tattalin arzikin ƙasar gaba ɗaya domin amfanin dukkan ’yan Najeriya.
A cewarsa, shirin sake fasalin ƙasar zai mayar da hankali kan muhimman fannoni huɗu, waɗanda suka haɗa da tsaro, ilimi, tattalin arziki da yanayin zamantakewa da siyasa.
Makinde ya ce za a iya kammala wannan shirin cikin shekaru huɗu.
Ya ce, “Mun taɓa samun wani shugaban ƙasa da ya riƙe shugabancin ƙasar na tsawon watanni 10, kuma ya samu damar kawo ƙarshen mulkin soja tare da kafa dimokuraɗiyyar da muke morewa a Najeriya a yau.
“Saboda haka, za mu iya sake tsara Najeriya. Za mu sake tsara tsarin tsaron ƙasar tare da samar da sabon tsarin tsaro. Za mu sake tsara ilimi domin bai wa ƙasar sabuwar hanya. Za mu sake tsara tattalin arzikinmu ta hanyar amfani da kimiyyar bayanai da dabarun tunani, tare da sake tsara yanayin zamantakewa da siyasa cikin shekaru huɗu. Wannan shi ne ajandarmu.”
Ya ƙara da cewa, “Saboda haka, idan kuka zaɓe ni shugaban ƙasa daga ranar 29 ga Mayun 2027, za mu kafa gwamnatin rikon ƙwarya ta haɗin kan ƙasa, wadda za ta haifar da sabbin shugabanni da sabuwar ajanda domin samun ci gaba mai ɗorewa a Najeriya.”
Makinde ya ce sakamakon zaɓen shekarar 2027 ba zai kasance bisa hasashen masana, masu gudanar da zaɓen ra’ayi ko yawan attajirai da ke bayan wani ɗan takara ba, sai dai bisa ra’ayin al’ummar Najeriya.
Ya kuma ce shugabanci na buƙatar kuzari, inda ya ba da misalin jadawalin ayyukansa cikin sa’o’i 24 da suka gabata, daga Ibadan zuwa Abuja, halartar taruka a Abuja, sannan yin tafiyar sa’o’i uku da rabi zuwa Lafia cikin dare, kafin ya ci gaba da ganawa da ’yan takara a shiyyar Arewa ta Tsakiya har zuwa ƙarfe 2:00 na dare.
Gwamnan ya soki abin da ya kira “voodoo economics”, wato wani tsari na tattalin arziki da bai gamsar da shi ba, a matakin gwamnatin tarayya.
Ya ce yayin da shekarar 2026 ke tsakiyar tafiya, matsalar rashin tsaro har yanzu babbar ƙalubale ce, musamman a yankin Arewa ta Tsakiya, amma ya ce bai ga wani tanadin kuɗi a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026 na sabbin rundunonin sojojin da aka sanar da kafa su ba.
Makinde ya kuma yi tambaya kan ko ƙarin kuɗaɗen da jihohi ke samu daga Asusun Tarayya ya haifar da wani gagarumin sauyi wajen yaƙi da yunwa a tsakanin al’umma.

No comments