A ranar Juma'a, 25 ga Satumba 2026, tawaga daga Ƙungiyar Ci gaban Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta ziyarci hedikwat...
A ranar Juma'a, 25 ga Satumba 2026, tawaga daga Ƙungiyar Ci gaban Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta ziyarci hedikwatar Babban Bankin Nijeriya (CBN) a Abuja.
Yayin ziyarar ta su, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ne da kan sa ya tarbi maziyartan daga ECOWAS, waɗanda ke ƙarƙashin jagorancin Dokta Sylla Kalilou, Kwamishinan ECOWAS mai kula da harkokin cikin gida, tare da Mista Dephue Yenpea Zuo, Kwamishinan Hukumar mai kula da harkokin tattalin arziƙi da noma.
Wannan ziyara dai ta zo daidai lokacin da Cardoso ya cika shekara uku daidai da naɗa shi Gwamnan CBN. A cikin waɗannan shekaru, Cardoso ya samar da tsare-tsaren bunƙasa tattalin arziki masu ɗimbin yawa.




No comments