Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za Mu Ɗaukaka Ƙara Kan Hukuncin Soke Mana Rijistar Jam'iyya – NDC

Jam'iyyar NDC ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta yanke, wanda ya soke hukuncin da ya bai wa h...



Jam'iyyar NDC ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta yanke, wanda ya soke hukuncin da ya bai wa hukumar zaɓen Nijeriya ta INEC umarnin yi mata rajista a matsayin jam'iyyar siyasa.

A wata sanarwa da shugaban jam'iyyar na ƙasa, Sanata Moses Cleopas Zuwoghe, ya fitar, NDC ta ce ba ta gamsu da hukuncin da kotun ta yanke bisa ƙarar da wata ƙungiya mai suna Peace Movement Party (PMP) ta shigar.

NDC ta ce PMP ba jam'iyya ce mai rijista ba, kuma ba ta cikin ƙungiyoyin da ke neman rajista a halin yanzu, saboda haka abin mamaki ne yadda kotun ta amince da buƙatarta ta sake duba hukuncin da ta riga ta yanke.

Jam'iyyar ta ce tun a watan Disamban 2025 kotu ta yanke hukuncin da ya ba ta damar kafa jam'iyya tare da umartar INEC ta yi mata rajista, wanda hukumar ta aiwatar.

"Tun daga lokacin, NDC ta gudanar da rajistar mambobi, tarukan jam'iyya daga matakin mazaɓa zuwa na ƙasa, tare da kammala zaɓen fidda gwani da kuma shiga zaɓukan cike gurbi da aka yi a jihohin Nasarawa da Enugu," in ji sanarwar

NDC ta ce ba wai kotun ba ta bayar da umarnin soke rijistar jam'iyyar kai tsaye ba ne, amma ta soke hukuncin da ya tilasta wa INEC yi mata rajista ne.

Saboda haka, ta ce ta umurci lauyoyinta su garzaya kotun ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin.

No comments