Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Wata Sabuwar Ƙungiyar Ta'addanci Mai Suna ‘Sai Malam’ Ta Bulla A Jihar Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana damuwa kan bullar wata ƙungiya mai alaƙa da ta’addanci mai suna Sai Malam a Ƙaramar Hukumar Argungu, tana m...




Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana damuwa kan bullar wata ƙungiya mai alaƙa da ta’addanci mai suna Sai Malam a Ƙaramar Hukumar Argungu, tana mai gargadin cewa ƙungiyar na iya zama babbar barazana ga tsaro idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.

Mai Bai Wa Gwamnati Shawara Kan Harkokin Tsaro na Jihar Kebbi, Kanal Danladi Ribah mai ritaya, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan tsaro da Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, DIG Suleiman Muhammad Abdul, ya gudanar a Birnin Kebbi.

Ribah ya bayyana cewa an fara gano ƙungiyar ne a Jihar Sokoto, inda jami’an tsaro suka yi nasarar dakile ayyukanta. Sai dai ya nuna damuwa cewa yanzu ƙungiyar ta bazu zuwa wasu sassan Jihar Kebbi.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta riga ta fara aiki tare da hukumomin tsaro domin dakile lamarin kafin ya rikide zuwa wata babbar matsalar tsaro.

“Babu wata shakka cewa mabiya ƙungiyar Sai Malam suna da yawa a Argungu. An fara gano wasu daga cikinsu a yankin Zuru, amma ba su da yawa kamar yadda ake gani a Argungu,” in ji Ribah.

Ya ƙara da cewa Gwamna Nasir Idris na ci gaba da gudanar da tarukan tsaro na wata-wata tare da shugabannin hukumomin tsaro, tare da samar musu da kayan aiki, tallafin kuɗi da sauran kayan gudanar da aiki domin yaƙi da masu garkuwa da mutane, Lakurawa, Mamudawa da sauran masu aikata laifuka.

Ribah ya bayyana cewa hare-haren Lakurawa kan Kebbi na fitowa ne daga Jihar Sokoto da kuma Jamhuriyar Nijar, yayin da wasu daga cikin ƙungiyar Mamudawa ke shiga jihar daga jihohin Kwara da Neja. Haka kuma, ya ce ‘yan bindiga na kai hare-hare daga Jihar Zamfara.

Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnati na ci gaba da sa ido sosai kan yanayin tsaro tare da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Rahotanni sun nuna cewa ƙungiyar Sai Malam ta fara aiki ne a wasu yankunan Jihar Sokoto kafin daga baya wasu rassa suka bazu zuwa wasu al’ummomi a Kebbi. An ce ayyukanta sun kai ga cafke jagoranta da wasu manyan mambobi a Sokoto, amma wasu daga cikin mabiyanta sun sake haɗuwa a yankin Argungu.

Gwamnatin jihar ta nuna fargabar cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, ƙungiyar na iya zama wata sabuwar barazana ga tsaron jihar.

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa ana danganta mambobin ƙungiyar da ayyukan tsafi, damfara da kuma jawo matasa masu rauni zuwa cikinta.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya shaida wa Daily Trust cewa ƙungiyar ta shafe kusan shekaru biyu tana aiki a wasu sassan jihar ba tare da jan hankalin hukumomin tsaro sosai ba.

A cewarsa, mutane da dama ba su ɗauki ƙungiyar da muhimmanci ba ne saboda ba ta gudanar da hare-hare irin na Lakurawa ko ‘yan bindiga.

“Su ma babbar barazana ce ga tsaro. Sai dai ba a san su da amfani da manyan makamai ba. Galibi suna amfani da wuƙaƙe, laya da wasu abubuwa masu haɗari wajen kai hari ko kashe waɗanda suka faɗa hannunsu,” in ji shi.

Wani mazaunin Argungu ya kuma tabbatar da cewa wasu daga cikin mambobin ƙungiyar suna zaune a cikin garin.

Ya ce galibi ana gane su ne ta hanyar irin tufafin da suke sawa da kuma baburan haya da suke amfani da su.

“Yawanci suna sanya gajerun wando da jalabiya, sannan suna hawa baburan da aka fi sani da ‘rubber-rubber’, waɗanda mafi yawansu ja ne. Suna da kuɗi sosai, kuma hakan na jan hankalin matasa da yawa zuwa gare su,” in ji shi.

Sai dai ya ce har yanzu ba a samu rahoton manyan hare-haren da suka kai a Argungu kamar yadda aka samu a wasu yankunan Sokoto ba.

A halin yanzu, Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro daga ƙungiyoyi daban-daban na masu tayar da ƙayar baya da masu aikata laifuka, musamman a yankunan Arewa.

Daga cikin fitattun ƙungiyoyin akwai Boko Haram da Daular Musulunci ta Yammacin Afirka (ISWAP), waɗanda har yanzu ke ci gaba da kai hare-hare a Arewa maso Gabas. Haka kuma ƙungiyoyin Ansaru da Lakurawa suna da tasiri a wasu sassan Arewa maso Yamma, yayin da ake danganta Mamudawa da ayyuka a jihohin Neja da Kwara.

Duk da ci gaba da gudanar da hare-haren soji da na jami’an tsaro domin murƙushe waɗannan ƙungiyoyi, har yanzu suna ci gaba da zama babban ƙalubale ga tsaron ƙasa.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun kiyasta cewa ayyukan ta’addanci da rikice-rikicen makamai sun yi sanadin mutuwar dubban mutane a Najeriya cikin shekaru goma da suka gabata.

Da yake mayar da martani a taron, Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, DIG Suleiman Muhammad Abdul, ya amince cewa yaƙi da miyagun laifuka na buƙatar kuɗaɗe masu yawa da kuma ci gaba da samun tallafi.

No comments