Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana nazarin matakan da za su ingant...
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana nazarin matakan da za su inganta tsarin jin daɗi da walwalar ma'aikatan da ke aiki a fannin yaɗa labarai a Nijeriya, a wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa aikin gwamnati da inganta gudanar da ayyukan yi wa jama'a hidima.
Daraktan Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a a Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya, Dakta Suleiman Haruna, ya faɗa a wata sanarwa ga manema labarai cewa ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin gudanar da rana ta biyu ta bukukuwan Makon Ma'aikatan Gwamnati na 2026 a Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya da ke Abuja.
Ya ce a wajen taron, an ba wasu jami'ai da ma'aikata takardun yabo domin girmama sadaukarwar su, ƙwarewar su da gudunmawar da suka bayar wajen bunƙasa ma'aikatar.
Da yake jawabi ga ma'aikatan ma'aikatar, Minista Idris ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya umurce shi da ya binciko hanyoyin da za a bi wajen inganta walwalar ma'aikatan fannin yaɗa labarai, yana mai tabbatar musu da cewa Gwamnatin Tarayya tana da aniyar ba da lada ga sadaukarwa, ƙwarewa da nagarta a aiki.
Ya ce: "Ina so na bayyana wannan a karon farko cewa muna aiki tare da Mai Girma Shugaban Ƙasa. Ya umurce ni da na duba abin da za mu iya yi, musamman ga ma'aikatan da ke fannin yaɗa labarai, domin inganta tsarin jin daɗin su. Ina tabbatar muku da cewa Mai Girma Shugaban Ƙasa zai tabbatar da hakan."
Ministan ya yaba da juriyar ma'aikatan gwamnati, sadaukarwar su da kishin ƙasa, yana mai bayyana su a matsayin ginshiƙin tafiyar da gwamnati da kuma abokan hulɗa masu muhimmanci wajen gina ƙasa.
Ya ce Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya tana da muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa, yaɗa sahihan bayanai da kuma taimaka wa 'yan ƙasa su fahimci manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
A cewar sa, ya kamata a yi amfani da bayanai a matsayin hanyar inganta haɗin kai, cigaba da haɗin kan ƙasa, ba wajen haddasa rarrabuwar kawuna ba.
Ya ƙara da cewa ma'aikatar za ta ci gaba da tallafa wa Ajandar Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hanyar ingantacciyar sadarwa da wayar da kan jama'a.
Ministan ya kuma bayyana wasu manyan nasarorin gwamnatin Tinubu, waɗanda suka haɗa da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, ƙaruwar kuɗaɗen shiga na jihohi, ƙarfafa ajiyar kuɗaɗen ƙasar waje, ci gaba da ayyukan gina ababen more rayuwa, da kuma faɗaɗa damar samun ilimi mai zurfi ta hanyar Asusun Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND).
Ya kuma bayyana cewa matakan tsaro da ake ci gaba da ɗauka tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa suna ci gaba da haifar da sakamako wajen magance matsalar rashin tsaro da inganta lafiyar jama'a a faɗin ƙasar nan.
Ministan ya buƙaci ma'aikatan da su ƙara jajircewa wajen riƙon amana, ƙwarewa da hidimta wa ƙasa ba tare da son kai ba, yana mai jaddada cewa cigaban ƙasa mai ɗorewa ya dogara ne da ƙwarewa da jajircewar ma'aikatan gwamnati.
"Babu wata ƙasa da za ta kai ga burinta ba tare da ƙwazon ma'aikatan gwamnati ba. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai iya yin komai shi kaɗai ba. Dole ne kowa daga cikin mu ya bayar da tasa gudunmawar wajen gina Nijeriyar da muke mafarki da ita."
Ministan ya yaba wa Babbar Sakatariyar Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya, Dakta Binyerem C. Ukaire, bisa kyakkyawan jagorancin ta, kulawar ta ga jin daɗin ma'aikata da kuma ƙoƙarin ta na inganta ingancin ayyukan ma'aikatar.
Tun da farko, a jawabin ta na maraba, Dakta Binyerem C. Ukaire ta bayyana ma'aikatan gwamnati a matsayin waɗanda ke tafiyar da harkokin gwamnati a bayan fage, inda ayyukan su ke tabbatar da ci gaba da gudanar da gwamnati da kuma isar da ingantattun ayyuka ga al'umma.
Ta ce an shirya bikin Makon Ma'aikatan Gwamnati ne domin karrama da yaba wa ma'aikatan gwamnati saboda irin muhimmiyar gudunmawar da suke bayarwa wajen bunƙasa ƙasa duk da cewa galibin aikin su na gudana ne ba tare da fitowa fili ba.
Ta kuma buƙaci ma'aikatan da su ci gaba da bin muhimman ƙa'idojin Tsarin Dabarun Aikin Gwamnatin Tarayya da Shirin Aiwatarwa (FCSSIP), waɗanda suka haɗa da inganci, ƙara yawan aiki, riƙon amana da kuma ba da hidima da ke sanya bukatun jama'a a gaba.
Babbar Sakatariyar ta tunatar da jami'an cewa su ne masu gina ƙasa kuma su ne wakilan kawo sauyi nagari, inda ta ce ayyukan da suke yi a kullum suna da tasiri kai-tsaye ga rayuwar 'yan Nijeriya.
Ta ce: "Duk wani aiki da kuke yi da kowane irin nauyin da kuka sauke yana taimakawa wajen bunƙasa ƙasa. Mu muhimman masu ruwa da tsaki ne wajen gina Nijeriya mai ƙarfi da inganci."
Taron ya samu halartar daraktoci, shugabannin sassa, manyan jami'an gudanarwa da sauran ma'aikatan ma'aikatar a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen bikin Makon Ma'aikatan Gwamnati na 2026.





No comments