Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jama’a Na Jin Yunwa, Ba Sai Kafafen Yaɗa Labarai Sun Faɗa Musu Ba – Atiku Ya Caccaki Tinibu

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kalaman da ke nuna cewa kafafen yaɗa labara...




Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kalaman da ke nuna cewa kafafen yaɗa labarai ne ke ƙara nuna tsananin matsalar rashin tsaro da wahalhalun tattalin arziki a ƙasar nan.

A cikin wata sanarwa da Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Laraba, Atiku ya ce ’yan Najeriya ba sa buƙatar rahotannin kafafen yaɗa labarai domin su fahimci irin matsalolin yunwa, hauhawar farashi da rashin tsaron da suke fuskanta a kullum.

“Atiku ya ce, ‘Ba sai ’yan jarida sun gaya wa ’yan Nijeriya cewa suna jin yunwa ba.’”

Ya ƙara da cewa uba da ke kwanciya cikin damuwa kan yadda zai samar wa iyalinsa abinci na gaba ba ya buƙatar karanta jarida domin ya tabbatar da cewa ana cikin wahala.

“Haka kuma uwa da yanzu take sayen kayan abinci da ninki uku ko huɗu na farashin da take sayensu shekaru biyu da suka gabata ba ta buƙatar kallon talabijin domin ta fahimci abin da hauhawar farashi ke nufi,” in ji shi.

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress a zaɓen shekarar 2027 ya bayyana cewa yunƙurin ɗora laifi kan kafafen yaɗa labarai saboda bayyana matsalolin ƙasa wata alama ce ta gwamnatin da ke ƙara nesanta kanta daga hakikanin rayuwar talakawa.

A cewarsa, miliyoyin ’yan Najeriya na fama da tashin farashin kayan abinci, raguwar ƙarfin saye, rashin aikin yi da kuma tabarbarewar yanayin rayuwa.

“Atiku ya ce nuna cewa ana ƙara yawan magana kan wahalhalun da ake ciki tamkar raina abubuwan da miliyoyin ’yan Najeriya ke fuskanta ne a rayuwarsu ta yau da kullum.”

Ya ce hakan kamar gaya wa jama’a ne cewa aljihunsu marasa kuɗi, tarin basussukan da ba a biya ba da kuma girke-girken da babu abin da za a dafa a cikinsu duk wani zato ne kawai.

Ya Taba Batun Rashin Tsaro

Atiku ya kuma yi martani ga kalaman wasu jami’an gwamnati game da matsalar rashin tsaro, yana mai cewa ’yan ƙasa suna ganin abin da ke faruwa da idanunsu ba tare da sai kafafen yaɗa labarai sun fassara musu ba.

Ya ce kafafen yaɗa labarai ba su ƙirƙiro kashe-kashen da ke faruwa a Benue ba, haka kuma ba su ƙirƙiro hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane a Plateau ba.

Ya kuma ce hare-haren ’yan bindiga a jihohin Zamfara, Katsina da Neja ba kirkirar kafafen yaɗa labarai ba ne, haka kuma matsalar garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa ba wani labari ne da aka ƙirƙira ba.

“Nijeriya Ta Zama Ƙasar Awa Takwas Ne Kawai?”

Atiku ya kuma soki ikirarin da ke cewa mutane da yawa na fadawa hannun masu garkuwa da mutane ne saboda rashin bin shawarar ’yan sanda ta kauce wa tafiye-tafiye da dare.

Ya tambayi ko hakan na nufin gwamnati ta amince cewa ’yan Nijeriya na iya gudanar da rayuwarsu cikin aminci ne na wasu ’yan sa’o’i kaɗai a rana.

“Shin Fadar Shugaban Ƙasa tana son ta ce ’yan Najeriya suna cikin aminci ne kawai na wasu sa’o’i kaɗan a rana? Shin wannan na nufin an mayar da mafi girman tattalin arziki a Afirka zuwa tattalin arzikin awa takwas, inda dole jama’a su rufe kasuwancinsu kuma su koma gidajensu da zarar rana ta faɗi?”shiji shi.

Atiku ya jaddada cewa alhakin kare rayuka da dukiyoyin jama’a yana hannun gwamnati ne, ba na talakawa ba.

Ya ce abin da ’yan Nijeriya ke tsammani daga gwamnati ba yawan nasihohi ba ne, illa ɗaukar matakai masu inganci domin magance matsalolin da suke fuskanta.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma kare rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa a tsarin dimokuraɗiyya, yana mai cewa aikin ’yan jarida shi ne bayyana gaskiya, isar da damuwar jama’a da kuma zama muryar talakawa.

“Dora laifi kan ’yan jarida saboda suna ba da rahoton rashin tsaro da wahala kamar zargin ma’aunin zazzabi ne saboda ya nuna mutum na da zazzaɓi,” inji shi.

A ƙarshe, Atiku ya bukaci gwamnatin Tinubu da ta mayar da hankali wajen magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro maimakon yin muhawara kan yadda jama’a ke kallon waɗannan matsaloli.

“Najeriya ba ta buƙatar karin bayani kan wahala. Najeriya na buƙatar mafita. nijeriya ba ta buƙatar darussa kan yadda ake kallon matsaloli. Nijeriya na buƙatar sakamako,” inji Atiku.

No comments