Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umarci bankuna da sauran cibiyoyin hadahadar kuɗi cewa su kulle dukkan asusu, mu’amaloli da kadarorin waɗans...
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umarci bankuna da sauran cibiyoyin hadahadar kuɗi cewa su kulle dukkan asusu, mu’amaloli da kadarorin waɗansu mutum shida da kamfanoni huɗu na hahahadar canjin kuɗi, wato 'Bureau De Change' (BDC) da aka sanya cikin jerin masu hannu wajen tallafa wa ta’addanci.
Wannan umarnin gaggawa ya biyo bayan takunkumin da gwamnatin Amurka ta ƙaƙaba wa Mukhtar Muhammad, wani ɗan canji da ke Legas, da wasu kamfanoni uku da ake zargin suna ƙarƙashin ikon sa.
CBN ya fitar da umarnin ne a cikin wata sanarwa mai lamba CMD/FCS/PUB/CIR/002/011 mai kwanan wata 24 ga Yuni, 2026, inda ya ce an sabunta jerin takunkumin wanda Nijeriya ta fara aiki da shi, tun ranar 18 ga Yuni, 2026, ya zama tilas ga dukkan cibiyoyin da ke ƙarƙashin kulawar sa.
Haka kuma CBN ya ce wannan matakin ya samo asali ne daga sabbin takunkumin da Kwamitin Takunkumin Nijeriya (NIGSAC) da Ofishin Kula da Kadarorin Kasashen Waje na Ma’aikatar Baitul Malin Amurka (OFAC) suka fitar ƙarƙashin Dokar Ƙarfin Iko, wato 'Executive Order 13224'.
Mutanen da aka saka cikin jerin waɗanda za a kulle wa kadarorin, sun haɗa da Muktar Muhammad Adamu, Babangida Muhammed, Adamu Hammajam, Abdullahi Umar Usman Ibrahim, Abubakar Adamu Chiroma, Yakubu Ogirima Ibrahim.
Haka kuma an sanya kamfanonin BDC guda huɗu da suka haɗa da Generation Currency Bureau De Change Limited, Manhattan Bureau De Change Limited, Nine to Nine Exchange Bureau De Change Limited da kuma Abbal Bako & Sons Bureau De Change Limited.
CBN ya umurci cibiyoyin hadahadar kuɗi cewa, “nan take su gaggauta ganowa tare da kulle duk wani kuɗi, kadara ko wata hanya ta tattalin arziki da ke ƙarƙashin mallaka ko ikon waɗanda aka sanya cikin jerin takunkumin.”
Wannan matakin ya zo ne bayan OFAC ta zargi Mukhtar Muhammad, wanda aka fi sani da Mukhtar Adamu Muhammad, da taimakawa wajen gudanar da hadahadar kuɗi da tura kuɗaɗe ga ƙungiyar ISWAP, reshen ƙungiyar 'Islamic State' da ke yammacin Afirka.
OFAC ta kuma ƙaƙaba wa kamfanonin Nine To Nine Exchange Bureau De Change Limited, Generation Currency Bureau De Change Limited, da Manhattan Bureau De Change Limited takunkumi, tana zargin an yi amfani da su wajen tura kuɗaɗen ga ƙungiyar.
Umarnin ya shafi duk wasu kamfanoni da ake da kashi 50 ko fiye, kai tsaye ko a fakaice na waɗanda aka sanya cikin jerin.
CBN ya ƙara gargaɗin cibiyoyin kuɗi da kada su samar da wani kuɗi, sabis na hadahadar kuɗi ko wata hanya ta tattalin arziki ga mutanen ko kamfanonin da aka sanya cikin jerin takunkumin.

No comments