Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana cewa Rundunar Sojin Ƙasa za ta ɗauki sabbin sojoji 28,000 aiki...
Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana cewa Rundunar Sojin Ƙasa za ta ɗauki sabbin sojoji 28,000 aiki domin ƙara ƙarfin rundunar wajen yaƙi da matsalolin tsaro da suka addabi sassa daban-daban na ƙasar nan.
Hafsan sojin ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Abuja yayin wani taron manema labarai da aka shirya gabanin bikin Ranar Sojin Nijeriya ta shekarar 2026 (NADCEL 2026).
Janar Shaibu, wanda Babban Jami’in Tsare-tsare da Manufofi na Rundunar Sojin Ƙasa, Manjo Janar Bamidele Alabi, ya wakilta, ya ce rundunar na ci gaba da amfani da dabarun zamani da fasahohin zamani domin ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro a faɗin ƙasar.
Ya bayyana cewa rundunar ta kafa sabon sansanin horas da masu neman shiga aikin soja a Amasiri Edda da ke Jihar Ebonyi domin faɗaɗa damar ɗaukar sabbin ma’aikata.
“A halin yanzu muna inganta dabarun tura jami’ai zuwa wuraren aiki tare da amfani da fasahar zamani domin ƙarfafa ayyukanmu na murƙushe dukkan nau’o’in laifuffuka a cikin ƙasar nan cikin sauri,” inji shi.
Ya ƙara da cewa ƙarfin ma’aikata yana da muhimmanci kamar kayan aiki da makaman da ake amfani da su wajen yaƙi da rashin tsaro.
“Saboda haka mun faɗaɗa tsarin ɗaukar ma’aikata ta hanyar kafa wani sabon sansanin horaswa a Amasiri Edda, wanda ya zama cibiyar horaswa ta uku da ke shirya matasa masu ƙoshin lafiya domin shiga Rundunar Sojin Ƙasa. Wannan zai taimaka wajen ƙara yawan jami’anmu.
“Da wannan mataki, ana sa ran Rundunar Sojin Ƙasa za ta ɗauki tare da horas da ƙarin sojoji 28,000 domin taimakawa wajen rage matsalolin rashin tsaro a faɗin Nijeriya,” ya bayyana.
Babban Hafsan Sojin ya kuma ce rundunar ta kafa ƙarin brigades da wasu sababbin rukunonin ayyuka domin ƙarfafa aikinta a wuraren da ake buƙata, tare da ci gaba da nazari kan tsarin rundunar domin cike gibin da ake gani a wasu yankuna da ke fuskantar sabbin barazanar tsaro.
Ya ce rundunar tana ci gaba da inganta ƙarfinta na aiki ta hanyar samar da sabbin kayayyakin yaƙi, na’urorin taimakon ayyukan soja da kuma ƙulla haɗin gwiwa da muhimman abokan hulɗa.
Janar Shaibu ya bayyana cewa tun bayan da ya hau kujerar Babban Hafsan Sojin Ƙasa na 25 watanni bakwai da suka gabata, rundunar tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro ta samu gagarumar nasara a fannoni daban-daban da suka haɗa da ayyukan tsaro, bunƙasa ababen more rayuwa, horar da ma’aikata, ƙwarewar aiki da kuma kyautata alaƙa tsakanin sojoji da fararen hula.
A cewarsa, waɗannan nasarori sun yi daidai da manufar jagorancinsa wadda ta mayar da hankali kan ci gaba da sauya Rundunar Sojin Ƙasa zuwa runduna mai ƙwarewa, mai saurin daidaitawa da yanayi, mai cikakken shiri domin yaƙi, kuma mai juriya wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya ɗora mata.
Ya jaddada cewa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro daban-daban ne ginshiƙin samun nasara wajen tunkarar ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta.

No comments