* Ya Umarci Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa Da Suke Son Yin Takara A 2027 Da Su Yi Murabus Kafin Ranar Juma'a Daga Khalid Idris Doya Gwamn...
* Ya Umarci Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa Da Suke Son Yin Takara A 2027 Da Su Yi Murabus Kafin Ranar Juma'a
Daga Khalid Idris Doya
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya rushe majalisar zartarwa ta jihar lamarin da ya kawo ƙarshen wa'adin aikin Kwamishinoninsa.
Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, shi ne ya sanar da wannan matakin a yayin ganawa da 'yan jarida a ranar Laraba, jimkaɗan bayan kammala zaman majalisar zartarwa ta jihar karo na 53.
Farfesa Njodi ya bayyana cewar gwamna Inuwa ya umarci dukkanin kwamishinonin da su miƙa ragamar ci gaba da gudanar da harkokin ma'aikatansu ga manyan sakatarorin ma'aikatun kafin ko ranar Juma'a 10 ga watan Afrilu, domin tabbatar da ci gaba da tafiyar da harkokin mulki da aiki yadda ya kamata ba tare da wani cikas ba.
Farfesa Njodi ya kuma sanar da cewa a yayin zaman da gwamnan ya jagoranta ya miƙa saƙon godiya ga kwamishinonin bisa jajircewa da suka nuna a ɓangaren aiki tare da bada nasu gudunmawar wajen ci gaban jihar da kyautata rayuwar al'ummar jihar.
Gwamnan ya musu fatan alkairi a rayuwarsu na gaba, ya yi fatan cewa da dama daga cikinsu za su ci gaba da bada gudunmawa ta ɓangaren ci gaban jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
Kazalika, a wani matakin kuma, gwamnan jihar ya umarci dukkanin sauran masu riƙe da muƙaman siyasa da suke sha'awar yin takarar siyasa a zaɓen 2027 a ke tafe da cewa su yi murabus daga muƙamansu kafin ko zuwa ranar Juma'a 10 ga watan Afrilu.
Matakin domin tabbatar da adalci da gaskiya tare kuma da bin dokoki da ƙa'idojin zaɓe ne.
Kwamishinonin da gwamnan ya sallama sun gode wa gwamnan bisa damar da ba su tare da nuna gamsuwarsu kan ƙoƙarin gwamnan wajen kyautata jihar Gombe.





No comments