Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Nijeriya Tana Samun Ci Gaba A Fannin Tsaro, Tana Nan Daram Duk Da Gargaɗin Amurka – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Nijeriya tana ci gaba da samun nasarori a fannin tsaro kuma tana nan daram, duk da matakin da Amurka ta ɗa...


Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Nijeriya tana ci gaba da samun nasarori a fannin tsaro kuma tana nan daram, duk da matakin da Amurka ta ɗauka na janye ma’aikatan ta daga ofishin jakadancin ta da ke Abuja.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce matakin da Amurka ta ɗauka wata hanya ce ta kariya bisa tsarin cikin gida, wanda hakan ba ya nuna ainihin yanayin tsaro na ƙasar baki ɗaya.

Ya ce: “Duk da cewa akwai wasu ƙalubalen tsaro a wasu yankuna, babu rushewar doka da oda gaba ɗaya, kuma mafi yawan sassan ƙasar nan suna cikin kwanciyar hankali.”

A cewar sa, hukumomin tsaro suna ci gaba da samun nasarori ta hanyar haɗin gwiwar sojoji, amfani da bayanan sirri, da kuma inganta aiki tare tsakanin hukumomi, wanda ke rage barazanar tsaro a yankunan da abin ya shafa.

Ya ƙara da cewa samamen baya-bayan nan sun daƙile ayyukan ƙungiyoyin masu aikata laifi tare da rage hare-haren da ake kaiwa, musamman a yankunan da suke fuskantar barazana.

“Hukumomin tsaron mu suna ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi, kuma sakamakon waɗannan ƙoƙari yana ƙara bayyana a fili,” inji shi.

Ministan ya jaddada cewa a buɗe Nijeriya take ga kasuwanci, yawon buɗe ido da zuba jari, yana mai cewa gyare-gyaren tattalin arziki suna ƙara ƙarfafa amincewar masu zuba jari da inganta matsayin ƙasar a idon duniya.

Ya bayyana cewa har yanzu abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa da masu zuba jari suna ci gaba da mu’amala da Nijeriya, abin da ke nuna amincewar su da kwanciyar hankali da makomar ƙasar.

Duk da amincewa cewa kowace ƙasa tana da ’yancin fitar da irin waɗannan shawarwari, Gwamnatin Tarayya ta buƙaci a riƙa ba da rahotanni masu daidaito da sababbin bayanai da ke nuna irin cigaban da ake samu.

Idris ya ce: “Muna kira ga abokan hulɗar mu na ƙasa da ƙasa da su ci gaba da tuntuɓar hukumomin Nijeriya domin samun cikakken bayani na halin da ake ciki a ƙasa,” inji shi.

Gwamnatin ta sake tabbatar da jajircewar ta wajen inganta tsaro, kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar wa da al'ummar duniya cewa Nijeriya ƙasa ce mai aminci da maraba ga kowa.
 

No comments