A wani gagarumin mataki na zamanantar da aikin ɗan sanda da rage raɗaɗin tsadar man fetur, Gwamnatin Tarayya ta miƙa wa Rundunar ’Yan Sandan...
Wannan tallafi, wanda ya fito ta hannun Asusun Tallafa wa ’Yan Sanda (NPF-TF) da kuma Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Motocin Gas da Lantarki (PI-CNG & EV), an miƙa shi ne a ranar Laraba a helkwatar rundunar da ke Abuja.
Sufeto Janar na ’Yan Sanda, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana jin daɗin sa ga wannan hangen nesa na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya bayyana cewa, Wannan canji zuwa amfani da makamashin gas da lantarki wani muhimmin mataki ne da zai sanya aikin dan sandan Nijeriya ya tafi daidai da yadda ake yi a ƙasashen da suka ci gaba.
“Za a yi amfani da waɗannan motoci ne domin inganta walwalar jami’ai da kuma sauƙaƙa zirga-zirgar su yayin gudanar da ayyukan tsaro.” Inji shi.
Rundunar tana shirin samar da cibiyoyin canza fasalin motoci (conversion centres) a cikin gida domin su rika gyara da kuma kula da motocin da kansu.
Shugabannin hukumomin biyu, a ƙarƙashin jagorancin Sakataren NPF-TF, Mohammad Sheidu, da Shugaban PI-CNG & EV, Barista Ismail Ahmed (OON), sun tabbatar da cewa wannan somin-tabi ne.
"Wannan mataki na ɗaya ne daga cikin babban shirin Gwamnatin Tarayya na sauya fasalin dukkan motocin aiki na ’yan sanda zuwa masu amfani da iskar gas (CNG). Wannan zai rage kudin da ake kashewa wajen sayen man fetur da kusan kashi 50% ko fiye da hakan."
Taron ya samu halartar manyan jami’ai daga hukumomin biyu, ciki har da CP Tony Emafale, Alhaji Sanusi Aliyu, da sauran wakilai daga bangaren kwamitin CNG na fadar shugaban kasa.
Wannan haɗin gwiwa wata hujja ce da ke nuna yadda Gwamnatin Tarayya take jajircewa wajen samar da ingantattun kayan aiki ga hukumomin tsaro ta hanyar amfani da fasahar zamani mai rahusa kuma marar illa ga muhalli.
Matakin zai ƙara wa rundunar karsashi wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan Nijeriya a wannan sabon zamani.


No comments