LABARI CIKIN HOTUNA: Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima; Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas; Ministan Labarai da Wayar...
LABARI CIKIN HOTUNA: Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima; Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas; Ministan Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris; tare da sauran manyan baƙi a wurin taron Makon Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (Nigerian Institute of Public Relations, NIPR), karo na 3, a Kaduna. An gudanar da taron ne ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, wanda kuma aka ba shi lambar girmamawa ta Gwarzon NIPR (Fellow).
Bikin ya gudana a sabon zauren liyafa na Birgediya Abba Kyari wanda aka ƙaddamar, a Gidan Sir Kashim Ibrahim, wato Fadar Gwamnatin Jihar Kaduna, a ranar 21 ga Afrilu, 2026.
No comments