Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don kare ’yan Nijeriya – Minista

   Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da tsaron ra...

  

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan Nijeriya a duk faɗin ƙasar nan.

Ministan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan rediyon BBC, inda ya yi tsokaci kan matsalolin tsaro na baya-bayan nan, ciki har da harin da aka kai Maiduguri.

Idris ya yi watsi da ra’ayin da wasu ke yaɗawa cewa hukumomin tsaron Nijeriya sun gaza, yana mai cewa ana ƙara ƙaimi domin hana aukuwar irin waɗannan hare-hare a gaba.

Ya ce: “Ba na ganin sun gaza. Ina ganin akwai buƙatar a ƙara ƙoƙari. Hukumomin tsaron Nijeriya suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa hakan ba zai sake faruwa ba.”

Ya bayyana cewa Maiduguri ta samu gagarumin cigaba a ɓangaren zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya tana ci gaba da ɗaukar matakai domin ƙarfafa tsaro a faɗin ƙasar nan.

A cewar sa,“Gwamnati tana mai da hankali sosai. Manufar tsare-tsaren gyaran da Shugaban Ƙasa yake aiwatarwa ita ce tabbatar da tsaron ’yan Nijeriya tare da hana sake aukuwar irin wannan lamari.”

Dangane da abubuwan da ke faruwa a duniya, musamman tashin hankalin Gabas ta Tsakiya, Idris ya ce a shirye Nijeriya take ta bayar da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiyar duniya, musamman a fannin makamashi.

Ya ce: “A ko yaushe Nijeriya a shirye take ta taimaka wajen tsaron makamashi a duniya. Duk abin da za mu iya yi don rage tashin hankali, za mu yi. Duniya tana buƙatar mai, kuma Nijeriya na nan."

Ministan ya kuma bayyana ziyarce-ziyarcen da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yake yi a ƙasashen waje a matsayin masu muhimmanci wajen ƙarfafa dangantakar Nijeriya da sauran ƙasashe.

Ya ce: “Wannan ziyara tana nuna tsohuwar dangantaka, alaƙar al’adu da alaƙar tattalin arziki tsakanin Nijeriya da Birtaniya. Muna fatan za mu ƙara ƙarfafa wannan dangantaka domin amfanin ƙasashen biyu.”

Idris ya ƙara da cewa gyare-gyaren da gwamnati take aiwatarwa suna fara inganta matsayin Nijeriya a idon duniya.

Ya ce: “Da gyare-gyaren da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar, mun fara ganin gagarumin sauyi a tattalin arziki.” 

Ya yi nuni da cewa hulɗar ƙasashen waje da Shugaban Ƙasa ke yi tana nuna yadda duniya take ƙara amincewa da Nijeriya.

A ƙarshe, ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyare tare da ƙarfafa tsaro domin tabbatar da cewa ’yan Nijeriya suna rayuwa da aiki cikin aminci.

No comments