Daga Ibrahim Muhammad, Kano Al'ummar Unguwar 'Yandodo a mazabar Hotoron Arewa ta Ƙaramar Hukumar Nasarawa ta jihar Kano sun yi kira...
Al'ummar Unguwar 'Yandodo a mazabar Hotoron Arewa ta Ƙaramar Hukumar Nasarawa ta jihar Kano sun yi kira ga Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf akan ya samar musu da ma'aikata da magunguna a Asibitin Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wada ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Nasarawa, Hon. Hassan Husaini ya gina aka ƙaddamar da shi kusan shekara ɗaya, amma har yanzu ba a soma aiki a ciki ba saboda rashin ma'aikata.
Injiniya Said Kamaludeen, shugaban Kwankwasiyya Elite na jihar Kano, wanda ya yi magana a madadin 'yan yakin ne ya bayyana hakan, inda ya ce mutanen yankin sun bayar da gudumlmawa sosai domin tabbatar nasarar Gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf da dukkan zabbabun yankin a lokacin zabe.
Daga nan ya yi nuni da cewa jagoran Kwankwasiyya na mazabar Hotoron Arewa, Hon. Shamsu Galadi ganin irin ɗimbin gudunmawar da suka bayar na samun nasara lokacin zabe ya sai ya tambayi abin da al'umma suka fi buƙata a Unguwar, suka ce Asibiti.
Ya ce wani lokacin cikin dare za a fito da marasa lafiya ko mata da za su haihu, kafin a je inda Asibiti yake an jigata, har ana samun rasa rai, amma idan aka sami Asibiti a unguwar, mutane da ƙafa ma za su iya takawa su je buƙatar su ta biya.
Hon. Said Kamaludeen ya ce jama'ar unguwa dama su suka tattara kuɗi sama da ₦6m suka samar da fili ta hannun Hon. Shamsu Galadi jagoran Kwankwasiyya na Hotoron Arewa, ya wuce musu gaba, ɗan majalisar tarayya na Nasarawa kuma ya gina musu.
Ya ce ɗan majalisar tarayyar ya miƙa wa Ƙaramar Hukumar Nasarawa, inda suka ce za su yi abin da ya kamata, su samar da ma'aikata da magunguna a ciki, amma yau wajen shekara ɗaya ke nan ba ta kawo ma'aikata ba, balle magani, yana rufe tun da aka ƙaddamar da shi.
Don haka sai Hon. Said Kamaludeen ya yi kira ga Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a irin kulawar sa da tausayin sa da taimakon al'umma da faɗa da cikawa, suna roƙon ya kawo musu ɗauki a kawo musu ma'aikata cikin gaggawa da za su ci gaba da aiki a Asibitin.

No comments