Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin ganawa da Shugaban Amurka Donald Trump domin tattauna zarge-zargen kis...
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin ganawa da Shugaban Amurka Donald Trump domin tattauna zarge-zargen kisan mabiyan addinin Kirista a Nijeriya da ake ta yayatawa a duniya.
Wannan bayani ya fito ne daga mai ba shugaban Æ™asa shawara kan yaÉ—a manufofi, Daniel Bwala, wanda ya wallafa sanarwa a shafinsa na X a ranar Asabar, yana mai cewa tattaunawar za ta gudana “a cikin kwanaki masu zuwa”, tare da mayar da hankali kan Æ™arfafa haÉ—in gwiwa wajen yaÆ™i da ta'addanci da tsattsauran ra'ayin addini a duniya.
A cewar Bwala, Tinubu da Trump na da “manufofi iri É—aya wajen yaÆ™ar ‘yan ta’adda da kowace irin barazana ga É—an Adam”, don haka tattaunawar ta taso ne don Æ™arfafa fahimtar juna kan batutuwan tsaro da addini.
Tattaunawar ta zo ne makonni bayan Trump ya yi suka ga Nijeriya, yana zargin cewa gwamnati ba ta kare Kiristoci daga hare-haren ‘yan ta’adda ba, har ma ya yi barazanar “yi amfani da Æ™arfi” idan har bai ga sauyi ba. Haka kuma ya yi barazanar iya dakatar da taimakon Amurka ga Nijeriya saboda batun tsaro.
Sai dai Bwala ya jaddada cewa duk shugabannin biyu tun da dadewa suna nuna kishin kawar da ta’addanci, inda ya nuna cewa lokacin gwamnatin Trump, Amurka ta amince da bai wa Nijeriya makaman yaÆ™i, waÉ—anda a yanzu gwamnatin Tinubu ta ce tana ci gaba da amfani da su wajen share sansanonin ‘yan ta’adda da kare fararen hula.
Ya Æ™ara da cewa Nijeriya ta tsaya tsayin daka wajen kare dukkan addinai, tare da tabbatar da cewa batun tsaro ya shafi ‘yan Æ™asa ba tare da bambanci ba, Musulmi ko Kirista, Arewa ko Kudu.
Ya zuwa yanzu, ba a bayyana ranar ganawar ba ko wurin da za ta gudana, sai dai fadar shugaban ƙasa ta ce shirye-shiryen hukuma na gudana tare da Amurka domin tabbatar da nasarar zaman.

No comments