A yayin da ake ta maganganu kan hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Nijeriya, wani sabon bincike ya bankaɗo yadda Musulmi ma suka daɗe suna...
A yayin da ake ta maganganu kan hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Nijeriya, wani sabon bincike ya bankaɗo yadda Musulmi ma suka daɗe suna fuskantar munanan hare-hare cikin masallatai da wuraren ibada tun daga 2009 zuwa 2025 — lamarin da bai samu isasshen kulawar duniya ba duk da yawan asarar rayuka.
Rahoton ya fito ne daga PRNigeria, wanda ya nuna cewa duk da tsauraran kalaman da tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya yi, na cewa wai ana “koren Kiristoci” a Najeriya, gaskiyar matakin tsaro a kasa ya fi dagulewa, domin Musulmi su ma na fuskantar kisa, fashe-fashe da hare-haren ta’addanci — musamman a arewacin Nijeriya.
Rahoton ya ce yawancin hare-haren da aka kai wa Musulmi an yi su ne a lokutan sallar safiya, azahar da dare, musamman a jihohin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma. Daga Boko Haram zuwa ISWAP da kuma ‘yan bindiga — duk sun taba kai irin wadannan hare-hare cikin masallatai.
Manyan Hare-Haren da Aka Kai wa Masallatai da Masu Ibada daga 2009–2025:
Agusta 11, 2013 — Konduga, Borno: An kashe Musulmai 44–46 yayin sallar Asuba.
Nuwamba 28, 2014 — Kano: Bam uku da harbe-harbe a Babban Masallacin Juma’a sun hallaka sama da mutum 80.
Yuli 17, 2015 — Damaturu: Hare-haren kunar bakin wake a sallar idi sun halaka mutum 50.
Oktoba 15, 2015 — Maiduguri: Hare-haren bam sun kashe mutane 42.
Nuwamba 21, 2017 — Mubi, Adamawa: Ɗan ƙunar baƙin wake ya hallaka mutum 50 a masallaci.
Oktoba 25, 2021 — Mazakuka, Jihar Neja: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 18 yayin sallar Asuba.
Nuwamba 5, 2023 — Funtua, Katsina: Hari a Maulidi ya hallaka mutum 20 tare da sace wasu.
Agusta 19, 2025 — Katsina: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 27 yayin sallar Asuba.
Waɗannan na ɗaya daga cikin mafi yawan hare-haren da aka tabbatar da su tsakanin 2009 da 2025.
Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soja kan Nijeriya bisa hujjar kare Kiristoci. Sai dai mahakonta na tsaro sun ce gaskiya ta fi karfin haka — domin Musulmi ma na cikin wadanda ake kashewa ba tare da bambanci ba.
Gwamnatin Nijeriya ta sha nanata cewa rikicin tsaro a kasar ya shafi kowa ne: Musulmi, Kiristoci, da sauran al’ummomi.
PRNigeria ta yi Allah wadai da duk wani kisan da ake yi cikin wuraren ibada — ko na Musulmi ko na Kiristoci — tana mai cewa kowane rai alfarma ne, kuma mutuwar kowanne mai ibada na bukatar tsananta hukunci da adalci ba tare da son kai ko nuna bambanci ba.

No comments