Rahotanni sun bayyana cikakkun bayanai game da wasu jami'an soji 16 da ake tsare da su bisa zargin hannu a yunkurin juyin mulki a Nijeri...
Rahotanni sun bayyana cikakkun bayanai game da wasu jami'an soji 16 da ake tsare da su bisa zargin hannu a yunkurin juyin mulki a Nijeriya, wanda ake cewa an yi nufi da hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar cewa daga cikin jami’an da aka kama, 14 daga ciki sojojin Æ™asa ne, ciki har da Brigediya Janar, Kanar, Lt. Kanar huÉ—u, Manjo biyar, Kaptan biyu da Laftanar É—aya. Haka kuma an kama jami’i É—aya daga rundunar ruwa da kuma wani daga rundunar saman Æ™asa daidai da matsayi na Manjo.
An ce mafi yawan jami’an da aka kama daga Infantry Corps suka fito — rukunin da ke shugabantar yaÆ™e-yaÆ™e a rundunar sojin Æ™asa. Wasu kuma sun fito daga sashen sadarwa da kayan yaÆ™i.
Bincike ya nuna cewa da dama daga cikin su sun yi karatu a Nigerian Defence Academy (NDA) a Ajin 56 (2004–2008), kuma guda shida daga cikinsu su ne aka fara kama tun farko.
Majiyoyin sun Æ™ara da cewa: 15 daga cikin jami’an daga Arewacin Nijeriya suka fito, yayin da daya yake daga Kudu maso Yamma.
Duk da haka, sojoji ba su fitar da cikakkun sunayen su ba har yanzu.
Zargin Makircin Kisan Manyan Jami'an Gwamnati
Wasu majiyoyi sun ce mahandaman sun yi niyyar kashe manyan jami'an gwamnatin tarayya ciki har da:
Shugaba Bola Tinubu
Mataimakin Shugaba Kashim Shettima
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio
Kakakin Majalisar Tarayya Tajudeen Abbas
da wasu mukarraban gwamnati.
Sai dai rundunar sojin ba ta tabbatar da wannan iƙirari ba.
Tuni dai Hedikwatar Tsaro ta Æ™aryata jita-jitar juyin mulkin, tana cewa jami’an da ake tsare da su, su na fuskantar binciken ladabtarwa ne, ba wai yunÆ™urin kifar da gwamnati ba.
Sauye-Sauyen Manyan Hafsoshi
Bayan faruwar lamarin, Shugaba Tinubu ya yi sabbin naÉ—e-naÉ—e a kan manyan Hafsoshin tsaro, inda ya maye gurbin su da:
CDS: Gen. Olufemi Oluyede
COAS: Maj. Gen. Waidi Shaibu
CAS: AVM Sunday Aneke
CNS: Rear Admiral Idi Abbas
Sai dai an bar Maj. Gen. Emmanuel Undiendeye a matsayin shugaban leƙen asiri na tsaro.
Farmaki a Gidan Tsohon Gwamnan Bayelsa
Binciken ya faÉ—aÉ—a, inda aka kai samame gidan Timipre Sylva, tsohon gwamna kuma tsohon minista. An kuma kama É—an uwan sa Paga Sylva da direban sa.
Sylva, wanda yake jinya a Landan, ya musanta zargin yana da hannu a juyin mulkin, yana mai cewa siyasa ce ta cin zarafi saboda shirin takarar gwamna a 2027.
Bincike na Ci Gaba
Majiyoyi sun ce har yanzu ana iya kama wasu jami’ai domin ana zargin akwai “babbar Æ™ungiya” da ke samun goyon bayan wasu masu faÉ—a a ji.
Hedkwatar tsaro har yanzu ba ta fitar da ƙarin bayani ba.

No comments